Fitaccen Dan Majalisa Ya Shiga Takarar Neman Gwamna a Jihar PDP, Ya Caccaki Gwamna Mai Ci

Fitaccen Dan Majalisa Ya Shiga Takarar Neman Gwamna a Jihar PDP, Ya Caccaki Gwamna Mai Ci

  • Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamna a jihar Edo, Hon. Anamero Dekeri ya nuna sha'awa
  • Dekeri wanda dan Majalisar Tarayya ne ya nuna sha'awar tasa ce a karkashin jam'iyyar APC mai mulkin kasa
  • Dekeri ya caccaki salon mulkin Gwamna Godwin Obaseki na jihar da cewa bai tabuka komai ba tsawon lokacin mulkinsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Hon. Anamero Dekeri da ke wakiltar mazabar Etsako a jam'iyyar APC ya nuna sha'awar tsayawa takara a jihar Edo.

Dekeri wanda mamban jam'iyyar APC ne ya caccaki Gwamna Godwin Obaseki kan irin mulkin da ya ke yi.

Dan Majalisar Tarayya ya tsaya takarar neman gwamnan jihar PDP
Anamero ya nuna sha'awar takarar ce a jam'iyyar APC. Hoto: Godwin Obaseki, Anamero Dekeri.
Asali: Facebook

Yaushe dan Majalisar ya nuna sha'awar tsayawa takarar?

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi shagube ga Betta kan alkawarinta na fitar da yan Najeriya miliyan 50 daga talauci

Dan Majalisar ya ce kwata-kwata mulkin Obaseki bai amfani mutanen jihar ba a bangaren ci gaban dimukradiyya da harkokin rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Anamero ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a Abuja a yau Alhamis 11 ga watan Janairu, cewar Politics Nigeria.

Ya bayyana muradinsa na tsayawa takara tare da tabbacin samun tikitin jam'iyyar a ranar 17 ga watan Faburairu.

Mene ya ke cewa game da mulkin Gwamna Obaseki?

Ya ce:

" Na tsaya a gabanku tare da neman bukata, sunana Hon. Anamero Dekeri ina tabbatar muku da sha'awar tsayawa takara a zaben Edo a 2024."

Yayin da ya ke magana kan kamun ludayin Gwamna Obaseki, Anamero ya ce:

"Ko makaho ne ya san cewa Gwamna Obaseki bai tabuka komai ba ganin yadda mutane ke shan wahala su na mutuwa.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi martani kan dakatar da Betta Edu, ya aika gagarumin sako ga Tinubu

"Duk wasu abubuwan more rayuwa sun ruguje, dukkan masana'antu don matasa babu su yanzu."

APC ta magantu kan shirye-shiryen zabe

A wani labarin, Gwamnonin jam'iyyar APC sun bayyana cewa a kullum a shirye suke don tunkarar ko wane zabe.

Gwamnonin sun bayyana haka ne a daren jiya Laraba 10 ga watan Janairu a Abuja bayan wata ganawa da suka ta sirri a tsakaninsu.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben cike gurbi da na jihohin Edo da kuma Ondo a wannan shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.