"Yadda Babangida da Obasanjo Suka Nemawa Buhari Alfarmar Takara a Zaben Shugaban Kasa"
- Ahmed Sani Yeriman-Bakura ya yi magana a kan yadda ya yafe takararsa a jam’iyyar ANNPP a lokacin zaben 2007
- Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya ce gwamnatin Olusegun Obasanjo ta fahimci zai hana jam’iyyar PDP yin nasara
- Yeriman-Bakura ya hakura da neman mulki har ta kai Janar Muhammadu Buhari ya iya tsayawa takara da PDP da ACN
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - A wata hira da aka yi da shi a Channels a ranar Juma’a, Ahmed Sani Yeriman-Bakura ya bada labarin abubuwan da suka faru a 2006.
‘Dan siyasar ya ce wasu manyan kasar nan suka shawo kan shi, ya fasa tsayawa takara saboda Muhammadu Buhari ya nemi mulkin Najeriyar.
Obasanjo ya hada Yarima da Babangida
Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya ce Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya hana shi tsayawa takarar shugaban kasa lokacin zaben 2007.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yariman Bakura yake cewa gabanin zaben da aka yi, yana cikin wadanda ake tunanin za su samu tikitin tsohuwar jam’iyyar nan ta ANPP.
A watan Disamban 2006, Sanata Yariman Bakura ya mike wajen taron zaben ‘dan takaran shugaban kasa, ya ce ya janyewa Muhammadu Buhari.
A karshe aka sanar da Muhammadu Buhari ne zai yi wa ANPP takarar shugaban kasa.
Yar’Adua v Buhari v Atiku a zaben 2007
The Cable ta ce a gefe guda, Marigayi Umaru Musa Yar’Adua ya samu takara a PDP, da aka yi zaben ya doke Janar Buhari da Atiku Abubakar.
A hirar da aka yi da shi, tsohon gwamnan ya ce kafin gangamin na ANPP, kungiyar ACF ta dattawan Arewa sun yarda a tsaida Buhari a 2007.
"Shugaban kasa Obasanjo ya tabbata ya kawo Janar Ibrahim Babangida a jirgin sama, wanda yana raye, ya roke ni in janye takara.
Shi ya na jam’iyyar PDP ni kuma ina ANPP.
A lokacin bayanai sun nuna masa, ina da goyon bayan ‘yan jam’iyya, in ban da na Kano da Katsina, na kyalewa Buhari a lokacin."
- Ahmed Sani Yeriman-Bakura
An rahoto shi ya ce IBB ya aiko Abdulkadir Kure da Attahiru Bafarawa su lallabe shi, daga baya sai ya fadawa Edwin Ume-Ezeoke ya janye.
Yarima ya ce shugabannin ANPP na duk jihohi suna tare da shi, gwamnati ta fahimci idan shi aka ba tuta, Yar’Adua ba zai kai iya labari ba.
Mulkin Yar'adua, Jonathan da Buhari
Kun taba samun labari cewa Marigayi Ummaru Yar’adua ya sanar da ofisoshin Ministocinsa ne bayan ya rantsar da su a shekarar 2007.
Sannu a hankali Shugaba Goodluck Jonathan ya rika rantsar da Ministoci a mulkinsa, akasin abin da Muhammadu Buhari ya yi.
Asali: Legit.ng