An Hada Tsohon Shugaba Buhari da Aiki a Katsina, Watanni 7 da Barin Kujerar Mulki

An Hada Tsohon Shugaba Buhari da Aiki a Katsina, Watanni 7 da Barin Kujerar Mulki

  • Kungiyar dattawan jihar Katsina za ta shirya wani zama na musamman da za a yi a shekarar nan
  • Aminu Abubar Danmusa ya shaidawa duniya wannan da ya kira taron manema labarai a Katsina
  • Shugaban kungiyar ya ce Muhammadu Buhari, gwamna da Sarakunan jihar Katsina za su zo taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Katsina - Tsohon shugaba Muhammadu Buhari da sarakunan Katsina da Daura za su halarci wani gagarumin taro a jihar Katsina.

Wata kungiyar dattawan jihar Katsina a karkashin jagorancin Alhaji Aminu Abubar Danmusa ta shirya taron a cewar Daily Trust.

Buhari
Muhammadu Buhari zai je taro a Katsina Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Kungiya ta gayyato Buhari

A ranar Laraba, Alhaji Aminu Abubar Danmusa ya kira manema labarai, ya shaida masu shirye-shiryen da ake yi domin taron bana.

Kara karanta wannan

Awanni da mutuwar gwamna da tsohon Shugaban Majalisa, an rasa mai mulki a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar ya ce daga cikin manyan wadanda aka yi nasarar gayyata zuwa wajen taron akwai Mai girma Muhammadu Buhari.

Sarakuna, Buhari za su albarka

"Mun samu gayyato Mai girma Muhammadu Buhari, tsohon shugaban tarayyar Najeriya, wanda zai halarci taron a matsayin babban bako na musamman.
"Hakan ya nuna muhimmancin tattaunawar da har Mai girma ya sa kan shi domin shiga cikin gagarumin taron.
"Bayan haka, Mai girma Malam Dikko Umar Radda, PhD, gwamnan jihar Katsina, zai zama mai masaukin baki, hakan ya nuna gudumuwar gwamnatin wajen goyon bayan wannan shiri.
"Mun kuma samu tabbacin Sarakunan Daura da Katsina da sauran manyan mutane, wannan ya nuna karbuwa da amincewar da tattaunawar ta samu."

- Alhaji Aminu Abubar Danmusa

Buhari zai taimaka a yaki shaye-shaye

Wani rahoton ya ce a taron shekarar nan, za a tattauna ne a kan illar shaye-shaye ga matasan Katsina domin ganin an shawo kan matsalar.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasar da su ka karbi mulki sanadiyyar mutuwar Gwamnonin jihohinsu a tarihi

Kungiyar za ta hada-kai da Muhammadu Buhari da sauran manyan Katsina domin ayi maganin lamarin nan da ya zama ruwan dare a yau.

Rikicin APC lokacin Buhari

Bayan shekaru uku da barin ofis, an rahoto cewa Adams Oshiomhole ya tona wadanda su ka yi sanadiyyar korarsa daga APC NWC.

Tsohon shugaban APC ya ce Muhammadu Buhari bai yi komai ba lokacin da za tunbuke shi, yana ji yana gani aka kawo Mai Mala Buni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel