Shugabancin Kasa: Yeriman Bakura ya magantu kan tsayawa takara a 2023 karkashin APC

Shugabancin Kasa: Yeriman Bakura ya magantu kan tsayawa takara a 2023 karkashin APC

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana cewa, shi cikakken dan jam'iyyar APC ne, kuma ba zai juya mata baya ba
  • A cewarsa, idan jam'iyyar APC ta tsayar da dan takara daga kudancin Najeriya zai janye kudurinsa na tsayawa takara
  • Duk da cewa, gwamnonin kudu sun yanke cewa dole a basu shugaban kasa daga yankinsu, Yerima ya ce yana kan bakarsa

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Yerima, ya ce zai janye takararsa ta kujerar shugaban kasa a 2023 idan har jam'iyyar APC mai mulki ta ba da tikitin zuwa yankin Kudu.

Yerima ya tattara hankalinsa gefe kan babban zaben shekarar 2023 yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Lahadi, Punch ta ruwaito.

Yerima ya ce bai ga dalilin da zai sa ya fice daga takarar ba, duk da kiran da gwamnonin kudu suka yi a taron su na karshe a Legas.

KARANTA WANNAN: Kaduna: Sojoji sun bazama daji don ceto sarkin Kajuru da iyalansa daga 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17,000 a sansaninsu na jihar Borno

Shugabancin Kasa: Yeriman Bakura ya bayyana matsayarsa kan takara a 2023 karkashin APC
Sanata Ahmed Sani Yerima | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta ruwaito Yerima na cewa:

“Eh, ina so in tabbatar muku da cewa da yardar Allah, idan ina raye, ni Sanata Ahmed Sani, na yi niyyar tsayawa takarar shugabancin kasa.
“Amma, ka gani, idan gobe jam’iyya ta (APC) ta zo ta ce mun ba da shugabancin kasa zuwa Kudu, ni, Yerima, zan bi ta. Daga nan zan san cewa shawara ce ta doka da kuma doka wacce ta hau kan dukkan mambobin jam’iyyar.”

Shin za ka iya barin jam'iyyar APC saboda wannan batu?

Da aka tambaye shi ko zai fice daga APC idan jam’iyyar ta fifita wani dan takarar shugaban kasa a kudu, don tabbatar da burinsa, Yerima ya ce ba a ba shi damar sauya sheka daga wata jam’iyyar zuwa waccan ba.

A kalamansa, cewa ya yi:

“Ka gani, ni mutum ne mai son addini sosai. A matsayina na Musulmi, na san cewa mulki na zuwa ne daga Allah, na farko. Idan Allah bai kaddara zan zama Shugaban kasa ba, wannan ba zai faru ba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Yadda 'yan bindiga suka sace shugaban wata kwaleji a jihar Zamfara

"Ban taba barin jam'iya ta ba. Na fara da APP (All Peoples Party); mun hade muka zama ANPP (All Nigerian Peoples Party). Daga baya, mun hade muka zama APC (All Progressives Congress).
"Don haka, ni memba ne na APC kuma ba ni da wata hanyar canza sheka daga jam’iyyata zuwa wata jam’iyyar.
“Don haka, da zarar akwai tsarin shiyya-shiyya, na san cewa lokacina ya wuce. Amma na tabbata cewa Allah da kansa ne zai yanke hukunci, ba mutane ba."

KARANTA WANNAN: Dr Isa Ali Pantami: Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijjah

Ganduje Ya Dakatar da Kungiyar Masu Bashi Shawari Na Musamman Saboda Rikicin Cikin Gida

A wani labarin, Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya dakatar da kungiyar manyan mataimaka ta musamman a Kano saboda rikicin shugabanci, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya ce gwammnati ta lura cewa abubuwan dake gudana a kungiyar suna dauke musu hankali daga asalin ayyukansu da kuma ba da gudunmawarsu ga gwamnati.

Kara karanta wannan

Gowon: Ku koma ga Allah, rashin tsaro zai kare a Najeriya nan kusa, ya bayyana mafita

Ya ce rashin jituwar da ke tsakanin shugabannin biyu na kungiyar ya haifar da rashin jin dadi da kunya ga gwamnati wanda in ba a kula ba, za ta iya lalata manufofi da burin da aka sanya kan SSA din.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel