Sarautar Kano: A Karshe, Abba Ya Fayyace Gaskiya Kan Umarnin Cafke Aminu Ado Bayero

Sarautar Kano: A Karshe, Abba Ya Fayyace Gaskiya Kan Umarnin Cafke Aminu Ado Bayero

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir ya bayyana babban dalilin ba da umarnin cafke Aminu Ado Bayero a jihar
  • Abba ya ce bayan tube Aminu Ado ya dawo jihar da neman ta da rigima da rashin zaman lafiya wanda ya zama dole a ba da umarnin
  • Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature shi ya bayyana haka yayin martani kan cece-kuce da ake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir ya fayyace musabbabin ba da umarnin kama Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Abba Kabir ya ce ya ba da umarnin ne bayan Aminu Ado ya dawo Kano da neman tada zaune tsaye a jihar.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Kwankwaso ya tona asirin masu zuga Aminu Ado, ya fadi shirinsu

Abba Kabir ya magantu kan umarnin cafke Aminu Ado Bayero a Kano
Abba Kabir ya bayyana musabbabin ba da umarnin kama Aminu Ado Bayero a Kano. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Kabir Yusuf, Masarautar Kano.
Asali: UGC

Abba ya magantu kan cafke Aminu Ado

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da kakakinsa, Sunusi Bature ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bature ya yi martani ne bayan wani mai suna Bala Ibrahim ya yi rubutu tare da zargin Abba Kabir da sakaci da kuma kama karya a mulki kan umarnin.

Ibrahim ya soki gwamnan da kuma zargin yadda giyar mulki ke rudarsa inda ya ke daukar matakai da ba su dace ba ciki har da umarnin cakfe Aminu Ado da rusau.

Martanin Abba Kabir kan Aminu Ado

A martaninsa, Bature ya kalubalanci Ibrahim inda ya ce anya ya fahimci gwamnati da yadda ake gudanar mulki kuwa?.

"Ba na son shiga lamarin shari'a, amma maganar rushe masarautu da Abba Kabir ya yi wanda aka yi gyaran fuska kan dokar masarautu ta 2019 wannan a fayyace yake."

Kara karanta wannan

Sallar layya: Masana sun bayar da hanyoyin cin nama ba tare da matsala ba

"Mayar da masarauu biyar zuwa guda daya shi ne burin mutanen jihar Kano."
"Dawo da Muhammadu Sanus II bai zo da mamaki ba saboda daman gwamnatin Abdullahi Ganduje ta tube shi ne ba domin Allah ba."
"Umarnin kama Aminu Ado kuma an yi ne domin mutanen Kano saboda bayan tube shi a sarauta ya dawo jihar wanda barazana ne ga zaman lafiya wanda ake korakin kiyaye wa har yanzu."

- Sunusi Bature

Ya ce Abba a matsayinsa na shugaban tsaron jihar ba zai nade hannu jiharsa ta tsunduma cikin matsala ba.

Abba ya ba mahajjata goron sallah

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya gwangwaje maniyyatan jiharsa da makudan kudi na goron sallah.

Abba ya ba mahajjatan jihar 3,121 riyal 100 domin gudanar da bukukuwan sallah cikin walwala a kasar Saudiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.