Littafin Tarihin APC Ya Jawo Tsohon Gwamna da Oshiomhole Sun Tonawa Junansu Asiri

Littafin Tarihin APC Ya Jawo Tsohon Gwamna da Oshiomhole Sun Tonawa Junansu Asiri

  • Ibikunle Amosun ya fitar da jawabi inda ya yi karin bayani a kan silar rikicinsa da Adams Oshiomhole a APC
  • Tsohon gwamnan ya karyata Sanatan na Edo ta Arewa, ya ce shi ya jawowa kansa rasa matsayinsa a NWC
  • Sanata Amosun ya ce zaben tsaida gwanin da APC ta shirya a 2019 ne ya ci Oshiomhole ba komai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Ogun - Ibikunle Amosun ya dauki lokaci ya yi kaca-kaca da Adams Oshiomhole a matsayin raddin bayanansa wajen kaddamar da littafi.

Ibikunle Amosun ya zargi Sanata Adams Oshiomhole da canza tarihi kan abubuwan da su ka faru a APC, Premium Times ce ta kawo rahoton.

Senator Ibikunle Amosun, Adams Oshiomhole
Ibikunle Amosun tare da Adams Oshiomhole Hoto: Senator Ibikunle Amosun, Adams Oshiomhole
Asali: Facebook

APC: Oshiomhole ya tsokano Amosun

Adams Oshiomhole ya ce Ibikunle Amosun da Dr. Kayode Fayemi su ka dage sai da aka tsige daga matsayin shugaban APC na kasa a 2020.

Kara karanta wannan

Atiku, Amaechi, Shekarau, Binani da jiga-jigan ‘yan siyasa da suka fi kowa asara a 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani jawabi na musamman da tsohon gwamnan na Ogun ya fitar, ya ce Oshimhole ya jefa APC cikin hadari a lokacin da ya zama shugaba.

Menene ya hadu Oshiomhole da Amosun fada?

Lokacin da ake shirin zaben 2019, Amosun ya nemi Abiodun Akinlade ya gaji kujerarsa, amma ‘dan takaransa bai samu tikitin APC ba.

Wasu suna ganin Oshiomhole ne ya yi ruwa da tsaki har jam’iyya ta tsaida Dapo Abiodun a Ogun, hakan ya fusata Amosun da mutanensa.

An yi kaca-kaca da tsohon shugaban APC

A jawabin da ya fitar, Amosun ya zargi Adams Oshiomhole da shirya zaben tsaida gwani mafi muni da aka taba gani tun da aka kafa siyasa.

Tsohon Sanatan ya ce irin zaben tsaida ‘yan takaran da Oshiomhole ya shirya da yake rike da majalisar APC NWC ne ya jawo ya bar kujerarsa.

Kara karanta wannan

Oshiomhole ya fadi mutane 3 da su ka kore shi daga shugabancin APC da karfi da yaji

Amosun: "Oshiomhole ya iya bakinsa"

Daily Trust ta ce tsohon ‘dan majalisar na Ogun ta tsakiya ya ba abokin rikicinsa shawarar ya tuna baya kafin ya rika bude bakinsa cikin jama'a

Amosun ya ce an sa dattawa da hikima a Afrika, bai kamata tsohon shugaban na APC ya kama sunayen mutanen da ba su yi laifin komai ba.

Fayemi ya je taron kaddamar da littafin APC

Ana da labari Kayode Fayemi ya ce dole Abdullahi Umar Ganduje su rika fadawa Bola Tinubu gaskiyar yanayin da al’umma su ke ciki.

Tsohon gwamnan na Ekiti ya bukaci Abdullahi Ganduje su zama masu fadan gaskiya ba yi wa Shugaban kasa zakin baki a fadar Aso Villa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel