Tsohon Gwamna ya Fadawa Ganduje Muhimmin Abin da Tinubu Yake Bukata a Wajensa
- Dr. Kayode John Fayemi ya yi jawabi wajen kaddamar da littafin da Salihu Mohammed Lukman ya wallafa a kan APC
- Jagoran na APC mai mulki ya bada shawara kowane shugaba ya nemi littafin ya karanta idan ana so jam’iyyarsu ta cigaba
- Fayemi ya bada shawarar cewa Abdullahi Umar Ganduje ya zama mai fadawa Mai girma Bola Tinubu idan ya shiga Aso Villa
Abuja - Kayode John Fayemi ya yi kira ga Abdullahi Umar Ganduje da ya kare manufofin jam’iyyar APC a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Tsohon gwamnan jihar Ekiti ya yi wannan kira ne a ranar Talata a lokacin kaddamar da littafin da Salihu Mohammed Lukman ya rubuta kan APC.
Kiran Kayode Fayemi ga Abdullahi Ganduje
Dr. Kayode John Fayemi ya ce shugaban APC yana bukatar ya rika fadawa shugaban kasa gaskiyar halin da al’umma su ke ciki a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin nauyin da ke wuyan Dr. Abdullahi Umar Ganduje shi ne ya zama yana kusanto da manufofin APC ga Mai girma shugaban kasa.
Masu yi wa Shugaban kasa Tinubu zakin baki
A jawabinsa, tsohon Ministan ya ce Bola Tinubu bai bukatar a cika kunnuwansa da irin labaran da ake yawo da su a fadar Aso Rock Villa.
Dr. Fayemi ya na cikin wadanda su ka karawa taron armashi, ya ce ya kamata duk abin da za ayi a gwamnati, a rika tafiya da jam’iyyar APC.
Jawabin Kayode Fayemi a gaban 'Yan APC
"Na ji dadi shugabanmu (na APC) yana nan. Wannan ce jam’iyyar da bai kamata ta zama ‘yar kallo wajen tsare-tsare ba.
Jam’iyyar nan ta zama mai gabatar da manufofinta. Jam’iyyar ta zama mai fadawa shugaban kasa martanin al’umma, ba abin da yake ji a Aso Villa idan an rufe shi ba.
Dukkanmu mun rike ofishin gwamnati, mun san yadda abin zai iya kasancewa."
- Kayode Fayemi
Ganduje a wajen kaddamar da littafin APC
An rahoto Fayemi yana mai cewa kyau duk ‘dan APC ya karanta littafin, wanda shi tuni tsohon gwamnan na jihar Kano ya karance shi tsaf.
A jawabinsa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce akwai bukatar ayi gyara da kyau a jam’iyyar APC mai mulki ta yadda za a kare hakkin talakawa.
Tinubu da shirin zaben 2027
A labarin da aka ji a baya, Ahmad Sani Yariman Bakura da wasu ‘yan adawar Bola Tinubu sun hakura za su bi bayan shi domin ya zarce a APC
Domin ganin jam'iyyar APC ta cigaba da mulki bayan 2027, an kafa kungiyar tsofaffin masu neman takara da za ta taimaki Shugaban Najeriyan.
Asali: Legit.ng