Lukman ya fallasa wani sirri da zagon kasa a jam'iyyar APC

Lukman ya fallasa wani sirri da zagon kasa a jam'iyyar APC

Darakta janar na kungiyar gwamnonin APC, Dr Salihu Lukman, ya zargi cewa akwai shirin mayar da Adams Oshiomhole tsohuwar kujerarsa ta shugabancin jam'iyyar APC.

Ya yi ikirarin cewa akwai kokarin da ake yi don zagon kasa ga kwamitin rikon kwarya na Mai Mala Buni.

DG Lukman a wani bayani da yayi a kan kwamitin rikon kwaryan, ya ce: "komai ana yin shi ne don ganin an juya siyasar cikin gida don samun yadda Oshiomhole zai haye kujerar shugabancin jam'iyyar."

Lukman, wanda babban mai adawa ne da salon Oshiomhole, ya ce daga cikin wani bangare na kokarin shine amfani da zaben Edo wajen cin zarafin shugabannin APC.

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun kama tsohon da ya sace yarinya yana bada haya don lalata da ita

"Amma wannan bai kamata ya zama matsala ba. Amma kuma, ganin cewa ana amfani da wasu salo ne don bacin suna da cin zarafi shugabannin jam'iyyar don wata manufa a zaben Edo ne abun takaici.

"Abun da ya fi zama na damuwa shine yadda Oshiomhole da wasu magoya bayansa basu son tunkarar zaben Edo a kan adalci. Ko bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin zaben adalci basu dubawa."

Lukman ya fallasa wani sirri da zagon kasa a jam'iyyar APC
Lukman ya fallasa wani sirri da zagon kasa a jam'iyyar APC Hoto: PM News
Asali: UGC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga kungiyar kamfen ta APC a jihar Edo da ta yi duk abinda ya dace kuma yake a kundin tsarin mulki don cin zaben.

Lukman ya yi kira ga kwamitin Buni da ta karfafa mahawarar cikin gida ba tare da cuzgunawa 'yan jam'iyyar ba ta yadda za ta ji ra'ayoyin jama'a.

Ya kara da cewa, a ware lokaci don sake duba yadda aka yi zabuka na Kogi da Bayelsa da kuma shirin zaben Edo da Ondo da ake yi.

KU KARANTA KUMA: Ina so in kwashe shekaru 90 kacal a duniya - Gwamna Ortom

Lukman ya yi kira ga kwamitin da ya fara duba diban 'ya'yan jam'iyyar wanda ahakan zai sa a kawo sauyi ga shugabancin jam'iyyar tun daga gunduma, kananan hukumomi, jihohi da kasa abaki daya.

Kamar yadda yace, akwai bukatar kafa kwamitin duba kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel