Abin da Tinubu Ya Fada Mana: Shugaban Tsagin Majalisar Jihar PDP Ya Fadi Dalilin Watsewarsu Zuwa APC

Abin da Tinubu Ya Fada Mana: Shugaban Tsagin Majalisar Jihar PDP Ya Fadi Dalilin Watsewarsu Zuwa APC

  • Shugaban tsagi na Majalisar jihar Rivers ya bayyana manyan dalilan da su ka saka su barin jam’iyyar PDP zuwa APC
  • Martins Chike Amaewhule wanda shi ne ya jagoranci ‘yan Majalisu 27 zuwa APC ya ce Shugaba Tinubu ya ba su tabbaci
  • Chike ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Port Harcourt a jiya Lahadi 17 ga watan Disamba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers – Yayin da rikicin jihar Rivers ke kara kamari, shugaban tsagi na Majalisar jihar, Martins Chike Amaewhule ya bayyana dalilin barinsu PDP.

Martins ya ce dukkan ‘yan Majalisar guda 27 da su ka sauya sheka daga PDP zuwa APC sun koma ne saboda rikicin siyasa a jihar, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

APC ta yi nasara yayin da kotu ta dakatar da INEC kan sake zaben 'yan Majalisu 27, ta tura gargadi

Shugaban tsagin Majalisar Rivers ya bayyana cewa Tinubu ya taka rawa wurin sauya shekarsu
Martins Chike ya bayyana abin da Tinubu ya fada masu kan sauya shekarsu. Hoto: Martins Chike, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Mene Martins ya ce kan Tinubu?

Chike ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Port Harcourt a jiya Lahadi 17 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan Majalisar ya ce da shi da sauran ‘yan Majalisar suna hujja a rikicin siyasar wanda hakan ya tilasta musu sauya shekar zuwa APC.

Vanguard ta tattaro cewa dan Majalisar ya ce sun sauya shekar ce saboda yadda Tinubu ke ayyukan alkairi a kasar, cewar Vanguard.

Ya ce:

“Mun sauya sheka kamar yadda kundin tsarin mulki na shekarar 1999 ya ba mu dama, ba mu saba doka ba.
“Mu na da hujjoji cewar akwai rikicin siyasa a jihar Rivers, mu na da dukkan damar da kuma ‘yanci na sauya sheka zuwa APC.”

Bayan rikicin siyasar a jihar, Amaewhule ya ce sun watsar da PDP din ce saboda yadda Shugaba Tinubu ke kawo abubuwan ci gaba a kasar.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu ya yi ritaya daga siyasa

Chike ya kara da cewa sun ji dadin yadda Tinubu ya nada ‘yan asalin jihar mukamai masu mhimmanci a kasar baki daya.

Wane yabo Martins ya yi kan Tinubu?

Ya kara da cewa:

“Mun roki shugaban kasa, tsohon shugaban kasa bai tabuka wani abu ba game da matsalar jhar Rivers.
“Mun roki Tinubu kuma ya ba mu tabbaci inda ya ce ku koma gida babu ruwa na da kabilancin siyasa, ni ba haka nake ba, wannan shi ne abin da shugaban ya fada mana.”

Ya ce bayan haka Tinubu ya himmatu wurin kawo abubuwan more rayuwa a yankin har babbar hanyar East-West da kuma matatar mai da ke Port Harcourt.

An rushe Majalisar jihar Rivers

A wani labarin, an wayi gari da labarin rushe Majalisar jihar Rivers yayin da rikicin siyasa ke kara kamari.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takun saka tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.