Gwamnoni 9 Da Aka Taba Tsigewa Daga Mulki a Sakamakon Hukuncin Kotun Koli a Tarihi

Gwamnoni 9 Da Aka Taba Tsigewa Daga Mulki a Sakamakon Hukuncin Kotun Koli a Tarihi

  • Kotun koli ta tsige gwamnoni ko masu jiran gado a jihohin kasar nan saboda samun matsala wajen zabensu
  • Wani lokaci ana tunbuke gwamnonin jihohin ne saboda an samu nakasa a takararsu ko ta mataimakansu
  • Jam’iyyun PDP da APC duk sun rasa mulki a irin haka, wasu lokutan kuma kujerun suna zama a jam’iyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A wannan rahoto, mun tattaru maku ‘yan siyasar da su ka rasa kujerar gwamnoni sakamakon hukuncin alkalan kotun koli.

A dalilin haka ne irinsu Rotimi Amaechi, Douye Diri da Hope Uzodinma su ka shiga ofis kamar yadda Vanguard ta kawo a wani rahoto.

Gwamnonin da aka tsige
Gwamnonin da aka tsige a kotun koli Hoto: @EmekaIhedioha, TVC
Asali: Twitter

1. Chris Ngige

A shekarar 2006, kotun koli ta soke nasarar da Dr. Chris Ngige ya samu tun a zaben 2003, alhali yana kokarin kammala wa’adinsa a jihar Anambra.

Kara karanta wannan

APC ta yi nasara yayin da kotu ta dakatar da INEC kan sake zaben 'yan Majalisu 27, ta tura gargadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Celestine Omehia

Bayan watanni kusan biyar yana mulki, kotun koli ta tunbuke Cif Celestine Omehia ta ce Rotimi Amaechi ne asalin ‘dan takaran PDP a Ribas a 2007.

3. Andy Uba

Bayan Chris Ngige a Anambra, kotun koli ta hana Andy Uba shiga ofis domin maida Peter Obi mulki. Wata guda da lashe zaben 2007, aka soke nasararsa.

4. Oserheimen Osunbor

Farfesa Oserheimen Osunbor yana cikin gwamnonin PDP da aka rusa zabensu a 2007, kotu ta ce Adams Oshiomhole ne ya lashe zaben jihar Edo.

5. Prince Olagunsoye Oyinlola

Wani gwamna da jam’iyyar PDP ta rasa a 2007 shi ne Prince Olagunsoye Oyinlola, shi me kotun koli ta tsige shi, ta bar jam’iyyar ACN nasara a Osun.

6. Olusegun Oni

A irin haka ne jaridar ta ce Dr. John Kayode Fayemi ya canji Segun Oni a jihar Ekiti. Alkalan babban kotun kasar sun soke zaben da aka yi a jihar.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya da Gandujiyya da sauran rigingimun siyasar da suka fi dadewa a Najeriya

7. Mukhtar Idris

Mukhtar Idris ya gama shirin zama gwamna sai kotu tayi hukunci APC ba ta gudanar da zaben tsaida gwani a Zamfara ba, a karshe PDP ta samu mulki.

8. David Lyon

Kamar a Zamfara, shi ma David Lyon ya lashe zabe da shirin zai yi mulki, sai kotu ta rusa nasararsa saboda samun mataimakinsa da badakalar takardu.

9. Emeka Ihedioha

Mai girma Emeka Ihedioha yana ofis aka tsige shi, abin mamakin shi ne Hope Uzodinma da INEC ta ce ya zo na hudu a zaben ya zama gwamnan Imo.

Zaben gwamnan Imo

Ana da labari jam'iyyar PDP ta fito tana ciki baki cewa lokaci kaɗan ya ragewa gwamna Hope Uzodinma a gidan gwamnatin jihar Imo.

A karshe dai Mai girma gwamnan ya samu gagarumar nasara a kan PDP da LP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng