Zaben 2019: Mukhtar Shehu Idris ya lashe tikitin Gwaman Zamfara a APC

Zaben 2019: Mukhtar Shehu Idris ya lashe tikitin Gwaman Zamfara a APC

Mun samu labari cewa shugabancin Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara da aka tsige kwanaki ta bayyana cewa Alhaji Mukhtar Shehu Idris ne yayi nasara a matsayin ‘Dan takarar Gwamna a karkashin APC.

Zaben 2019: Mukhtar Shehu Idris ya lashe tikitin Gwaman Zamfara a APC
Wakala da sauran 'Yan takara sun sha kasa hannun Mukhtar a APC
Asali: Depositphotos

Daily Trust ta rahoto cewa Mukhtar Shehu Idris wanda yayi nasara a zaben da aka yi a makon jiya ne ya sake samun tikitin APC a karshen makon da ya gabata. Alhaji Lawali M. Liman ne ya gudanar da sabon zaben.

Sai dai kuma Uwar Jam’iyya ta rusa shugabancin wadanda su ka gudanar da zaben tun kwanaki sannan kuma Jam’iyyar ta gaza gudanar da wani sabon zabe kafin lokacin da Hukumar zabe na INEC ta bada ya shude.

KU KARANTA: APC ba ta da ‘Yan takara a Jihar Zamfara a zaben 2019 - Inji PDP

A zaben da bangaren Liman wanda ke tare da Gwamna Abdulaziz Yari ya gudanar. Shehu Idris ya samu kuri’a sama da 310, 000 yayin da Sanata Kabiru Marafa ya zo na biyu. Marafa ya samu kuri’a 54,607 ne a zaben.

Alhaji Mahmuda Aliyu Shinkafi ya ci 5,514, Ibrahim Wakkala Muhammad kuma ya samu 517; Alhaji Sagir Hamidu Gusau ta tashi da kuri’a 102; Hon. Aminu Jaji ya zo na uku a zaben inda ya samu kuri’u har 12, 039.

Birgediya Janar Mansur Dan Ali (rtd) wanda shi ne Ministan tsaro ya tashi da kuri’a 292 ne kacal, Sauran ‘Yan takarar dai sun hada da Alhaji Abu Magaji 340 da kuma Alhaji Dauda Lawal Dare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel