An kafa tarihi: David Lyon na APC ne sabon zababben gwamnan Bayelsa - INEC
Hukumar gudanar da zabe ta kasa wato INEC ta alanta da Cif David Lyon na jam'iyyar All Progressives Congress APC matsayin zakaran zaben gwamnan da aka gudanar ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2019.
David Lyon ya lashe kuri'un kananan hukumomi shida yayinda babban abokin hamayyarsa na PDP, Duoye Diri, ya kashe kananan hukumomi biyu.
Nasarar Lyon ta karya tarihin mulkin PDP a jihar na tsawon shekaru 20 tun 1999 da aka dawo da emokradiyya Najeriya.
Baturen zaben jihar Bayelsa, Farfesa Faraday Orumwense, ya bayyana sakamakon cewa Lyon ya samu jimillar kuri'u 352,552 yayinda Diri ya samu kuri'u 143,172.
Kananan hukumomin da APC ta lallasa PDP sun hada da Brass; Nembe; Ogbia, Southern Ijaw, Ekeremor da Yenagoa yayinda PDP ta samu Sagbama da Kolokuma/Opokuma.
Kalli jerin sakamakon:
Karamar hukumar Sagbama APC - 7,831 PDP - 60339 Nuw
karamar hukumar Nembe APC-83,041 PDP- 874 Nuw
Karamar hukumar Kolokuma/Opokuma APC - 8,934 PDP - 15,360
Karamar hukumar Brass APC - 23,831 PDP - 10,410
Karamar hukumar Yeneguwa APC - 24,607 PDP - 19,184
Karamar hukumar Ogbia APC - 58, 016 PDP - 13, 763
Karamar hukumar Southern Ijaw APC - 124,803 PDP - 4898
Karamar hukumar Ekeremor APC - 21,489 PDP - 18,344
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng