Duk da Alaka Mai Tsami a Tsakani, Gwamnan PDP Ya Taya Wike Murna, Ya Tura Masa Sako Mai Jan Hankali

Duk da Alaka Mai Tsami a Tsakani, Gwamnan PDP Ya Taya Wike Murna, Ya Tura Masa Sako Mai Jan Hankali

  • Yayin da alaka ke kara tsami, Gwamna Fubara na jihar Rivers ya taya Nyesom Wike murnar bikin haihuwarsa
  • Fubara ya taya murnar ce a yau Laraba 13 ga watan Disamba a shafinsa na X duk da matsalar da ke tsakaninsu
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takun saka tsakanin gwamnan da mai gidansa kan jagorancin jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara ya taya mai gidansa, Nyesom Wike murnar cika shekaru 56 da haihuwa.

Fubara ya ta ya Wike murnar ce a shafin X a yau Laraba 13 ga watan Disamba, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Shugaba Tinubu ya umarci majalisar ta miƙa mulki ga mataimakin gwamnan APC

Gwamnan PDP ya yi ta maza inda ya taya mai gidansa murna
Fubara ya taya Wike murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Hoto: Nyesom Wike, Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Mene Fubara ya ce kan Wike?

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takun saka tsakanin gwamnan da mai gidansa kan jagorancin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wallafawar, Fubara ya ce ya taya mai gidansa murnar zagayowar ranar bikin haihuwarsa.

Ya ce da shi da iyalansa duka har ma jama'ar jihar Rivers su na taya tsohon gwamnan murna inda ya masa fatan alkairi.

Fubara ya ce:

"Ina taya mai gidana murna, Dakta Barista Nyesom Ezenwo Wike, Ministan Abuja kuma tsohon gwamnan Rivers murnar cika shekaru 56 a duniya.
"Mai girma, da ni da matata da kuma sauran jama'ar jihar Rivers mu na taya ka murna da addu'ar ubangiji ya karo shekaru masu albarka."

Wace alaka ce tsakanin Wike da Fubara?

Wannan na zuwa ne bayan rikicin da ke tsakanin Gwamna Fubara da uban gidansu, Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Gobara ta kama ofishin gwamnan jihar Borno

Rikicin ya jawo babbar matsala a Majalisar jihar inda aka samu farraka a tsakanin mambobin Majalisar.

Hakan nema ya saka 'yan Majalisu 27 daga cikin 32 a jihar ficewa a jam'iyyar PDP zuwa APC.

An rushe Majalisar jihar Rivers

A wani labarin, an wayi garin yau Laraba 13 ga watan Disamba da rushe Majalisar jihar Rivers.

Hakan ya tilasta mambobin Majalisar zama a wani wuri na musamman da aka kebe a gidan gwamnatin jihar.

Wannan na zuwa ne bayan rikicin da ke tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike na kara tsami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.