An Aike da Sako Ga Tinubu Yayin da Yan Majalisa Masu Biyayya ga Wike Suka Shirya Tsige Fubara
- Gwamnan Siminialayi Fubara yana fuskantar barazana a matsayinsa na gwamnan jihar Rivers
- Ƙungigar Ijaw Congress ta yi zargin Nyesom Wike da magoya bayansa a majalisar dokokin Rivers sun kammala shirin tsige Fubara daga muƙaminsa
- Sai dai ƙungiyar ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya sa baki kan lamarin domin Fubara ya mayar da hankali kan mulkin jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Port Harcourt, jihar Rivers - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya samu muhimmin saƙo daga ƙungiyar Ijaw National Congress (INC) kan rikicin siyasar jihar Rivers.
Rikicin siyasar jihar Rivers ya fara ne biyo bayan yunƙurin tsige gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara da ƴan majalisar dokokin jihar suka yi.
Ƙungiyar ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya shiga tsakani a rikicin da ke tsakanin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da wanda ya gaje shi, Gwamna Fubara, inji rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane kira suka yi wa Shugaba Tinubu?
Shugabannin na Ijaw sun buƙaci Tinubu da ya dakatar da Wike da magoya bayansa kan yunƙurin da suka yi na korar Fubara a matsayin gwamnan jihar Rivers.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da INC ta yi Allah wadai da abin da ta yi wa lakabi da goyon bayan da hukumomin tsaro na ƴan majalisar dokokin jihar ke yi wa Wike.
INC, a wata sanarwa ɗauke da sa hannun shugabanta, Farfesa Benjamin Okaba, a ranar Litinin, 11 ga watan Disamba, ta ce tana mamaki cewa duk da shiga tsakanin da Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki a baya, Wike ya duƙufa wajen ganin an tsige Fubara.
"Ya mai girma shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, muna roƙonka da ka sake gargaɗin Mista Wike da hukumomin gwamnatin tarayya da ke ƙoƙarin jefa jihar Ribas cikin hatsarin rashin zaman lafiya, da su shiga taitayinsu." A cewar Okaba.
Ƴan Majalisar Dokokin Rivers Sun Koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan majalisar dokokin jihar Rivers na jam'iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.
Ƴan majalisar waɗanda ke biyayya ga tsohon Gwamna Wike sun sauya sheƙar ne a yayin da rikicin siyasar jihar ke ƙara ƙamari.
Asali: Legit.ng