Jigon NNPP Ya Fadi Dalili 1 da Ya Sa Masu Ruwa da Tsakin Jam'iyyar Suka Tabbatar da Korar Kwankwaso
- Wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP sun yi ikirarin cewa ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaben Fabrairu 2023, Rabiu Musa Kwankwaso ne matsalar jam’iyyar
- Masu ruwa da tsakin dai sun tabbatar da korar Kwankwaso, wanda yake jigo ne a siyasar yankin Arewacin Najeriya
- A wata hira da Legit.ng, wani jigo a jam’iyyar NNPP, Adekunle Aderibigbe, ya ce ba ya tunanin masu ruwa da tsaki a yankin Arewa maso Gabas za su sake haifar da rikici
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Kano, jihar Kano - Adekunle Aderibigbe, jigo a jam’iyyar NNPP a jihar Legas, ya yi magana kan jaddada korar Rabiu Musa Kwankwaso da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a yankin Arewa maso Gabas suka yi.
Jigon ya bayyana cewa hakan da suka yi wata sabuwar dabara ce suka zo da ita domin kawo gyara a jam'iyyar.
Aderibigbe, a zantawarsa da Legit.ng, ya ce matakin da jam’iyyar NNPP ta yi a yankin Arewa maso Gabas na da nufin kawo gyara ne, ba wai domin tada zaune tsaye ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPP tana aiki don magance rarrabuwar kawuna - Aderibigbe
Tsohon ɗan takarar majalisar dokokin jihar Legas ya ce sanar da korar Kwankwaso na da nufin ganin shi (Kwankwaso) ya fara yin gyare-gyaren da ya dace ga ɗaukacin ƴaƴan jam’iyyar a faɗin Najeriya domin su ba da cikakken goyon baya don cigaba da riƙe nasarar Kano.
A kalamansa:
Sanarwar da masu ruwa da tsaki na NNPP a yankin Arewa maso Gabas suka yi bayan taron su, ba wai kawai ya nuna rashin amincewarsu da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ba ne, amma har da tabbatar da goyon bayansu ga wanda ya kafa jam'iyyar NNPP, Dr. Boniface Aniebonam."
An gabatar da diyar Tinubu a matsayin sarauniyar Najeriya a wajen bikin daurin aure, bidiyon ya yadu
"Sun fahimci muhimmanci ganin cewa kowane masu ruwa sa tsaki sun haɗa kansu da samar da daidaito domin ci gaban jam'iyyar. Abin da suka yi a gani na domin gyara ne ba wai domin su kawo rikici ba."
"Sanar da korar Kwankwaso da suka yi sun yi ne domin su sanya shi ya fara yin gyare-gyaren da suka dace ga dukkanin ƴaƴan jam'iyya da yankuna domin bayar da goyon bayan da ya dace wajen riƙe nasarar Kano."
An Bukaci DSS Ta Gayyaci Kwankwaso
A wani labarin kuma, kun ji cewa an buƙaci rundunar ƴan sandan fararen kaya da ta gaggauta gayyatar Rabiu Musa Kwankwaso domin ya amsa tambayoyi.
Ƙungiyar yaƙin da ta'addanci ta NCAT ce dai ta yi wannan kiran saboda zanga-zangar da aka yi a Kano, wacce a cewarta akwai hannun Kwankwaso a ciki.
Asali: Legit.ng