An Yi Rashi: Tsohon Sakataren NUPENG, Frank Kokori Ya Yi Bankwana da Duniya Yana da Shekara 80

An Yi Rashi: Tsohon Sakataren NUPENG, Frank Kokori Ya Yi Bankwana da Duniya Yana da Shekara 80

  • Allah ya yi wa tsohon babban sakataren ƙungiyar NUPENG, Cif Frank Kokori rasuwa yana da shekara 80 a duniya
  • Jigon na jam’iyyar APC a jihar Delta, Kokori ya rasu a ranar zagayowar ranar haihuwarsa a wani asibiti mai zaman kansa da ke Warri da ƙarfe 1:30 na dare
  • Duk da samun kulawar manyan baƙi da jami’ai a lokacin rashin lafiyarsa, ciki har da Gwamna Sheriff Oborevwori, ciwon Kokori ya ƙara ta'azzara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Cif Frank Kokori, tsohon babban sakataren ƙungiyar man fetur da iskar gas ta Najeriya (NUPENG) ya rasu yana da shekaru 80.

Kokori, jigo a jam’iyyar APC a jihar Delta, an kwantar da shi a asibiti sakamakon ciwon koda da ya yi fama da shi a watan da ya gabata.

Kara karanta wannan

A Karshe, Jam'iyyar PDP ta fara ɗaukar matakan farfaɗowa daga bugun da ta sha a zaben 2023

Frank Kokori ya yi bankwana da duniya
Frank Kokori ya rasu yana da shekara 80 a duniya Hoto: @DSGovernment
Asali: Facebook

Ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke Warri da misalin karfe 1:30 na daren ranar Alhamis 7 ga watan Disamba, wanda ya yi daidai da zagayowar ranar haihuwar sa, kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar da rasuwar Kokori

Jaridar Punch ta kuma ruwaito cewa, mataimakinsa na musamman Atawada Barry Oke ne ya bayyana rasuwar Kokori.

A cewar Oke, lafiyar tsohon shugaban ƙungiyar kwadagon ta sake taɓarɓarewa ne a ranar Litinin, 4 ga watan Disamba, saboda ya kasa yin mu’amala da mutanen da ke kusa da shi saboda tsananin ciwo.

Kokori na cikin ƴan gwagwarmayar ranar 12 ga watan Yuni. Marigayin ya bayar da gudunmuwa ga ƙungiyar da ke adawa da soke zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yuni wanda aka yi imanin Moshood Kashimawo Olawale (MKO) Abiola ne ya lashe zaɓen.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar Labour Party ta caccaki Peter Obi, bayanai sun fito

Yadda Frank Kokori ya yi fama da ciwon ƙoda

Kokori, mai shekara 80 kuma fitaccen ɗan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Delta, ya rasu ne wata guda ɗaya bayan ya bayyana rashin kulawa da yadda aka yi watsi da shi a yayin da yake fama da ciwon ƙoda a asibitin Mount Horeb dake Warri.

Oladipo Diya Ya Yi Bankwana da Duniya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban rundunar sojojin Najeriya, Janar Oladipo Diya, ya yi bankwana da duniya.

Diya wanda tsohon mataimakin shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha ne, ya bar duniya yana da shekara 78.

Asali: Legit.ng

Online view pixel