Lauyoyi Sama da 200 Sun Shirya Tsaf Don Tabbatar da Abba Gida-Gida Ya Yi Nasara a Kotu

Lauyoyi Sama da 200 Sun Shirya Tsaf Don Tabbatar da Abba Gida-Gida Ya Yi Nasara a Kotu

  • Lauyoyi a Najeriya sun taru don yiwa Abba Kabir Yusuf gata a kotu kan karar da ya shigar na neman hakkinsa a gaban kuliya
  • An tsige Abba a zaman kotun kararrakin zabe da kuma kotun daukaka kara, har yanzu ba a kammala zaman kotun ba
  • Wani jigon APC ya gama hango abin da zai faru a kotun koli, ya ce akwai yiwuwar APC ta yi nasara duba da wasu ka’idojin doka

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Kaduna - Kimanin lauyoyi 200 ne suka sadaukar da kansu domin taimakawa Abba Kabir Yusuf, gwamnan Kano, wajen samun nasara a karar da ya shigar a gaban kotun koli.

Lauyoyin da ke karkashin kungiyar “Abba Kabir Yusuf Volunteer Lawyers Forum” sun fito ne daga jihohin Arewa 19 da kuma babban birnin tarayya (FCT), TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Waye zai yi nasara a kotu? Jigon siyasa ya hango abin da zai faru a shari'ar Abba da Gawuna

Da yake jawabi ga manema labarai a Kaduna ranar Lahadi, Yusuf Ibrahim, mai magana da yawun lauyoyin, ya bukaci shugaba Bola Tinubu da ya tabbatar da cewa kotun koli ta yanke hukunci ba tare da ya tsoma baki ba.

Lauyoyi za su taimaki Abba Kabir Yusuf
Lauyoyi 200 sun shirya yiwa Abba aiki | Hoto: Yusuf Gawuna, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyoyin sun dage cewa, hukuncin kotun daukaka kara da ya bayyana Yusuf Gawuna, dan takarar jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya yi nasara rashin adalci ne, rahoton Channels Tv.

Lauyoyi sun hango lam’a a dokar zabe

Lauyoyin sun kuma bukaci a sake yin aiki kan dokar zabe, inda suka kara da cewa bai kamata a bar kotu ta bayyana wani dan takara a matsayin wanda ya lashe zabe ba.

Sun bayyana cewa:

“Hatsarin da ke tattare da hakan shi ne, idan har wannan yanayin ya ci gaba ba tare da an dinke shi ba, to babu bukatar tara mutane tare da kada kuri’u a zabuka.”

Kara karanta wannan

ASUU ta tubure, ta ce bata amince a ba dalibai rance ba, ga abin da take so a yi

Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da jiran abin da zai biyo baya a kotun koli don tabbatar da hukuncin da za a yi na karshe.

APC ce za ta yi nasara, inji jigon siyasa

A wani labarin, kotun koli za ta yanke hukunci kan karar da Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano da Caleb Mutfwang na jihar Filato suka shigar, inda suke kalubalantar hukuncin kotunan zabe da kuma hukuncin kotun daukaka kara.

A baya an kori gwamnonin biyu tare da ba abokan hamayyarsu gaskiya duba da wasu hujjojin da aka gabatar a gaban alkalai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel