Abin da Ya sa Mutanen Kwarai Ba Za Su Taba Samun Mulki a Najeriya Ba – Tsohon Gwamna

Abin da Ya sa Mutanen Kwarai Ba Za Su Taba Samun Mulki a Najeriya Ba – Tsohon Gwamna

  • Abubuwa sun yi tabarbarewar da Muazu Babangida Aliyu yake ganin siyasa ta zama sana’ar mutanen banza a yau
  • Tsohon gwamnan ya ce an maida samun mulki hanyar neman dukiya ta yadda mutumin kirki ba zai iya shiga ba
  • Dr. Muazu Babangida Aliyu yake cewa tun daga sayen fam zuwa zaben tsaida gwani, an yi waje da mutanen kirki

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Muazu Babangida Aliyu wanda ya yi shekaru takwas ya na gwamna a jihar Neja, ya koka game da tsarin zabe a Najeriya.

This Day ta rahoto Dr. Muazu Babangida Aliyu ya na cewa rashin gaskiyar da ake yi wajen takara ya ware mutanen kwarai a siyasa.

Tsohon Gwamna
Tsohon Gwamna, Muazu Babangida Aliyu a taron NIPR Hoto:Muhammad Hashim Suleiman
Asali: Facebook

Babangida ya ce siyasa ta koma kudi

Kara karanta wannan

Matashi ya nuna yadda wayar iPhone dinsa ta makale a tukunya bayan ya yi kuskure wajen girki

A irin yadda ake tafiya a halin yanzu, Muazu Babangida Aliyu ya nuna ba za ta yiwu mutane masu gaskiya su iya samun takara ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon na PDP ya yi wannan magana ne da aka gayyace shi zuwa taron kungiyar NIPR wanda aka shirya ranar Asabar a Kaduna.

Babangida Aliyu yake cewa daga cikin abubuwan da ke kawo cikas shi ne yadda wasu ke nuna shakku a tsarin damukaradiyyan.

Irinsu Cif Olusegun Obasanjo sun fara nuna sam tsarin bai aiki yadda ya kamata a Afrika.

An rahoto Dr. Babangida Aliyu ya na kokawa kan yadda siyasa ta koma harkar kashewa da neman kudi a maimakon hidima.

Matsayar Muazu Babangida Aliyu

"Tsarin ya lalace ta yadda ba za ta yiwu mai gaskiya, mutumin kirki, ya yi takara a Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya kadu bayan bankado wata badakala, ya sha alwashin daukar mataki

Kudin sayen fam, masu zaben ‘dan takara su na ganin lamarin kamar hanyar samun kudi ne, su bi duk masu neman kujera su karbi kudi, duk da sun san mutum daya za su iya zaba.
A karshe wanda ya fi bada kudi shi zai samu takara. Saboda yadda ake gudanar da zabenmu, an yi watsi da halayen kwarai a siyasa. Talauci ya jawo ledar taliya ko atamfa za ta sa mutum ya saida shekaru hudu a rayuwarsa."

- Muazu Babangida Aliyu

Za a ja da Shugaba Tinubu a kotu?

Ifeanyi Araraume ya ce Bola Tinubu ya sabawa doka da ya nada shugabannin NNPCL alhali shari’arsa da gwamnatin tarayya ta na kotu har gobe.

Sanatan da ya kai gwamnatin Muhammadu Buhari kotu ya nuna nadin sababbin shugabannin NNPC bai da madogara ta fuskar dokar kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel