Ba Zai Yiwu Alkalai 3 Su Sauya Zabin Miliyoyin Mutane Ba a Kotu, Tsohon Shugaban Kasa Ya Magantu

Ba Zai Yiwu Alkalai 3 Su Sauya Zabin Miliyoyin Mutane Ba a Kotu, Tsohon Shugaban Kasa Ya Magantu

  • Cif Olusegun Obasanjo ya yi martani kan yadda alkalai ke sauya ra’ayin mutane miliyoyi a hukuncin kotun zabe
  • Tsohon shugaban kasar ya ce hakan rashin adalci ne mutane su yi zabe amma wasu mutum uku ko hudu su sauya hukuncin
  • Obasanjo ya bayyana haka ne yayin da kotu ta kwace kujerun gwamnoni uku a cikin mako daya kacal

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya nuna damuwa kan yadda ake yanke hukuncin zabe a kasar.

Obasanjo ya ce bai kamata alkalai uku kacal su sauya ra’ayin miliyoyin ‘yan Najeriya ba a lokacin zabe, Legit ta tattaro.

Obasanjo ya yi martani kan hukuncin kotu da ta kwace kujerun gwamnoni 3 a mako
Obasanjo ya soki tsarin yadda alkalai ke sauya hukuncin zabe. Hoto: Cif Olusegun Obasanjo.
Asali: Twitter

Mene Obasanjo ke cewa kan kotun zabe?

Kara karanta wannan

Bayan sauka mulki, Muhammadu Buhari ya faɗi manufa 1 tal da ta sa ya canza takardun naira a Najeriya

Tsohon shugaban ya ce bai kamata ba a bai wa alkalai irin wannan karfin iko ba yayin yanke hukuncin zabe, Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olusegun ya bayyana haka ne yayin martani kan hukunce-hukuncen kotu musamman a cikin ‘yan kwanakin nan.

Wannan na zuwa ne bayan kotu ta kwace kujerun gwamnoni uku a Najeriya wanda dukkansu ‘yan jam’iyyun adawa ne.

Gwamnonin sun hada da Abba Kabir na jihar Kano da Dauda Lawal na Zamfara sai kuma Caleb Mutfwang na jihar Plateau.

Obasanjo ya ce:

“Na yarda da ko wane tsari na dimukradiyya mu ke da shi, amma bai kamata alkalai uku ko hudu su sauya ra’ayin mutane miliyoyi ba.
“Ina ga bai kamata hakan ya kasance ba ace mutane miliyan 10 ko tara sun yi zabe, kawai wasu mutane na zaune su sauya hukuncin zaben.”

Kara karanta wannan

Yadda muka sha kaye a zaben 1998 domin na ki bai wa INEC cin hanci, Obasanjo

Obasanjo ya kara da cewa babban abin takaici shi ne babu mai sauya wannan hukunci na mutane uku ko hudu da su ka sauya zabin al’umma.

Kotu ta rusa zaben Gwamna Dauda na Zamfara

A wani labarin, kotun daukaka kara ta rusa zaben Gwamna Dauda Lawal Daure na jihar Zamfara inda ta ayyana shi a mastayin wanda bai kammala ba.

Kotun ta umarci sake zabe a wasu kananan hukumomi uku da ta ke zargin an tafka magudi da rashin bin ka’ida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel