Muazu Babangida Aliyu zai zama Shugaban kasa a 2019 - Ayegbajeje
- Wani Fasto yace tsohon Gwamnan Neja zai zama Shugaban kasa
- Adeyemi Aiyegbajeje yace Babangida Aliyu zai mulki kasar nan
- Limamin yace Dr. Babangida Aliyu ya cancanci ya rike Najeriya
Labari ya zo mana cewa wani Babban Malami na addinin Kirista a kasar nan ya bayyana wanda zai karbi mulkin kasar daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019.
Wani Limami da ke Legas ya hanga ya duba cewa tsohon Gwamnan Jihar Neja watau Dr. Muazu Babangida Aliyu ne zai zama Shugaban kasa a 2019. Fasto Adeyemi Ayegbajeje yace Shugaba Buhari da kan sa zai mikawa tsohon Gwamnan ragama.
KU KARANTA: An fara sulhu tsakanin Ganduje da Kwanakwaso
Faston yace da ya duba, an nuna masa cewa Babangida Aliyu ne zai cigaba da mulki daga inda Shugaba Buhari ya tsaya. Babban Faston yace tsohon Gwamnan ya cancanci shugabancin kasar nan ganin irin kwarewar sa da basirar sa na aiki.
Ayegabajeje wanda ke zaune a Legas ya bayyanawa Jaridar Newscroll abin da ya gano kwanaki. Faston yace tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne zai yi kutun-kutun na ganin tsohon Gwamnan na Jihar Neja ya samu mulkin kasar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng