Daga Karshe An Bayyana Dalilin da Ya Sanya PDP Ta Kasa Hukunta Wike da Yan G-5
- Shugaban riƙo na jam'iyyar PDP ya bayyana dalilin da ya sanya har yanzu jam'iyyar ba ta hukunta waɗanda suka ci dunduniyarta ba
- Umar Iliya Damagum ya bayyana cewa ba zai hukunta kowa ba saboda yanzu ƙoƙarin sasanci yake ba sake ruguza jam'iyyar ba
- Ya yi nuni da cewa yanzu ƙoƙari yake ya haɗa kan jam'iyyar tare da sasanta waɗannda ke rikici a tsakaninsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban riƙo na jam’iyyar PDP, Umar Damagum, ya ce kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) ƙarƙashin jagorancinsa ba zai dakatar ko korar duk wani mamban jam'iyyar mara biyayya ba, cewar rahoton The Punch.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ta PDP suka yi kira ga Damagum da ya hukunta tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike da wasu da dama bisa zargin cin dunduniyar jam’iyyar a lokacin babban zaɓen 2023.
Damagum, wanda ya yi watsi da hakan a lokacin da yake jawabi ga kungiyar PDP Mobilisers Group a Abuja, ya bayyana cewa kwamitin NWC ya amince da kafa kwamitin da zai duba tare da sulhunta dukkan mambobin da suke rikici da juna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban jam’iyyar ya ce jam’iyyar ta fi sha’awar sasantawa da shigo da mutane da yawa a cikin jam’iyyar fiye da hukunta duk wani da ake zargin ya ci dunduniyar jam’iyyar, wanda a cewarsa hakan ka iya ruguza jam’iyyar.
Ya ce:
"A koyaushe suna gaya muku mutanen nan ba sa yin abin da ya dace. Amma a lokacin da kake kan shugabanci, akwai dokokin da kake bi, kuma waɗannan dokokin duk da cewa suna yi maka zafi, ba ka amfani da su, ba don komai ba, amma sai don kada ku lalata gidan.
Meyasa ba za a hukunta wadanda suka ci dunduniyar PDP ba?
Damagum, wanda ya yarda cewa ƴaƴan jam’iyyar da dama suna da hannu dumu-dumu a cikin ayyukan da suka saɓa wa jam’iyya a matakai daban-daban, ya cigaba da cewa:
"Idan na ce a fara dakatarwa, zan dakatar da mutane da dama saboda suna da hannu a cikin ayyukan da suka saba wa jam’iyya. Don haka, don Allah ku yi haƙuri da mu. Mun ƙudiri aniyar haɗa kan wannan jam’iyya tare da gudanar da ita."
"Lokacin da sabon shugaba ya zo, zai iya yanke shawarar dakatarwa ko korar kowa. Amma ni kaina a matsayina na mai son wannan jam’iyya, wanda ya fara wannan jam’iyya, ina ganin muna bukatar hatta waɗanda ke wancan ɓangaren su dawo."
Sabon Rikici Ya Kunno a PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kan wanda zai cigaba da riƙe jam'iyyar.
Atiku Abubakar yana ta ƙulla-ƙulla kan yadda zai cigaba da riƙe jam'iyyar domin yin takara a 2027, sai dai yana fuskantar ƙalubale daga wasu jiga-jigan jam'iyyar.
Asali: Legit.ng