Zaben Edo: Wike Ke Daukar Nauyin Takarar Gwamnan da Philip Shaibu Ya Fito? Jigon PDP Ya Fadi Gaskiya

Zaben Edo: Wike Ke Daukar Nauyin Takarar Gwamnan da Philip Shaibu Ya Fito? Jigon PDP Ya Fadi Gaskiya

  • Akwai raɗe-raɗin cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ne ya ɗauki nauyin takarar Philip Shaibu
  • Wani jigon jam’iyyar PDP, Earl Osaro Onaiwu, ya yi watsi da waɗannan raɗe-raɗin tare da bayyana su a matsayin tsabagen ƙarya
  • Onaiwu ya buƙaci mazauna jihar Edo da magoya bayan jam’iyyar da kada su yarda da jita-jitar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Earl Osaro Onaiwu, wanda shi ne Daraktan-Janar na farko na ƙungiyar gwamnonin PDP, ya yi magana kan batun cewa Nyesom Wike ne ya ɗauki nauyin tsayawa takarar da Philip Shaibu ya yi.

Onaiwo ya buƙaci magoya bayan jam'iyyar da su yi watsi da rahotannin masu cewa ministan na birnin tarayya Abuja ne ya ɗauki nauyin takarar da Philip Shaibu ya fito na neman gwamnan jihar Edo a 2024.

Kara karanta wannan

Tsige gwamnan Kano: Bode George ya caccaki hukuncin kotun daukaka kara

Philip Shaibu ya fito takarar gwamnan Edo
Philip Shaibu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Edo Hoto: Nyesom Ezenwo Wike/Rt. Hon. Comrade Philip Shaibu
Asali: Facebook

Onaiwu, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba, ya jaddada cewa ɗaiɗaikun mutane na amfani da sunan Wike don cimma wata manufa ta siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jaddada cewa Wike ya wuce irin waɗannan abubuwa kuma ya kamata a bar shi ya mai da hankali kan ayyukansa na Ministan babban birnin tarayya Abuja.

Kamar yadda PM News ta ruwaito, Onaiwu ya ce:

"Ina so in bayyana a fili cewa waɗannan raɗe-raɗin ba su da tushe kuma ya kamata duk ƴaƴan PDP a jihar Edo su yi watsi da su."

Wacce shawara Onaiwu ya ba ƴaƴan PDP?

Ya buƙaci ƴaƴan jam’iyyar PDP na jihar Edo da su mayar da hankali wajen gina jam’iyya mai ƙarfi da haɗin kai, tare da jaddada muhimmancin haɗin kai wajen ganin an samu nasara a zaɓen gwamna na 2024 a jihar.

Kara karanta wannan

Rigima ta ɓalle, Mataimaki Shaibu ya ɗara caccakar Gwamnan PDP kan zaben jihar na 2024

Onaiwu ya ce:

"Muna buƙatar mu mayar da hankali wajen gina ƙaƙƙarfar jam’iyyar PDP a Edo. Kada mu bari mu shagala da raɗe-raɗi da jita-jita."

Onaiwu ya yi kira ga ɗaukacin ƴaƴan jam’iyyar PDP na jihar Edo da su tsaya tsayin daka da sadaukar da kai ga ƙimar jam’iyyar yayin da ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da kwarewa da sanin ya kamata a cikin rahotannin su.

"Kada mu bari ƴan siyasa su yi amfani da mu wajen cimma manufarsu ta siyasa." A cewarsa.

Shaibu Ya Fito Takarar Gwamnan Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya bayyana aniyarsa ta neman takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

Shaibu ya sha alwashin cewa babu mai dakatar da shi a zaben da za a gudanar a shekarar 2024 da za a gudanar a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel