Farfesa Jega Ya Kawo Hanyoyin da Za a bi Kafin a Iya Gyara Hukumar INEC a Najeriya

Farfesa Jega Ya Kawo Hanyoyin da Za a bi Kafin a Iya Gyara Hukumar INEC a Najeriya

  • Attahiru Jega ya halarci wani taro na musamman da kungiyar kasashen Turai da Yiaga Africa su ka shirya
  • An yi zaman ne domin a tattauna yadda za inganta harkar zabe a kasar, sai aka gayyato tsohon shugaban INEC
  • Jega ya kawo shawarar raba INEC, a gyara dokar zabe kuma a duba wadanda ake ba mukamai a hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Attahiru Jega ya yi kira ga ‘yan majalisar tarayya su barka hukumar zabe ta kasa (INEC) saboda a iya shirya zabuka da kyau.

Farfesa Attahiru Jega ya yi wannan kira ne a wajen wani taro da Yiaga Africa da kungiyar EU su ka shirya, Daily Trust ta kawo rahoton.

Kungiyoyin turan da na matasan sun shirya taron ne da hadin-kan kwamitocin majalisar dattawa da wakilan tarayya kan harkar zabe.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban INEC, Jega Ya Soki Hukuncin Zaben Kano, Ya ba Tinubu Shawara

Zaben 2023
Jami'ar INEC a lokacin zaben 2023 Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jega yana so ayi garambawul ga INEC

A jawabin da ya gabatar, Attahiru Jega ya ce zai yi kyau a kacancana hukumar ta INEC, a cewarsa kwaskwarimar za ta inganta zabuka.

Bayan haka, ya nuna sai an yi dauki matakin haramta sauya-shekar da ‘yan siyasa ke yi, Daily Post ta rahoto shi yana kokawa kan hakan.

Farfesa Jega yana ganin ba daidai ba ne a zabi mutum a wata jam’iyya, kwatsam sai a ji ya yi tsalle ya koma jam’iyya musamman mai-ci.

A hana sauya-sheka bayan zabe

A cewarsa doka ta yi bayani karara cewa muddin mai rike da mukami ya canza sheka, zai rasa kujerar sai dai idan ana rikici a jam’iyyar.

"Daga 2011 zuwa 2022, an yi kokari sosai wajen gyara hakar zabe. Watanni da rantsar da wata gwamnati, an fara gyara dokokin zabe.

Kara karanta wannan

Jami’an Tsaro sun cika ko ina, NNPP da APC sun hakura da zanga zanga a Kano

Garambawul da aka yi wa dokar zabe a 2022 shi ne mafi kyau, amma za a iya ingantawa.
Dole mu duba sha’anin hakkin yin zabe, jam’iyyun siyasa, zaben tsaida gwani, shari’a a kotu, tsaro, sannan a wayar da kan al’umma."

- Attahiru Jega

Farfesan ya nanata kiran da yake yi na sake duba wadanda aka nada REC a INEC, ya kuma ce jam’iyyu su rika hattara wajen tsaida takara.

PDP ta fara shiryawa zaben 2027

A makon nan ne rahoto ya zo cewa an fara lissafin wanda zai zama sabon shugaban jam'iyyar PDP bayan an yi waje da Dr. Iyorchia Ayu.

Sunayen tsofaffin Gwamnoni sun fara yawo, ana zargin Nyesom Wike yana da ’yan takaransa a jam’iyya idan an tashi shirin yin zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng