Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Shari’ar Zaben Kakakin Majalisa a APC, Ta Bayyana Mai Nasara

Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Shari’ar Zaben Kakakin Majalisa a APC, Ta Bayyana Mai Nasara

  • Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari’ar zaben kakakin majalisar jihar Gombe da aka rusa
  • Kotun ta tabbatar da nasarar Abubakar Luggerewo na jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Akko ta Tsakiya a jihar
  • Kotun har ila yau, ta rusa hukuncin kotun zabe da ta bai wa Bashir Gaddafi na jam’iyyar PDP nasara

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe – Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar kakakin majalisar jihar Gombe, Honarabul Abubukar Luggerewo.

Kotun ta yanke hukuncin ne a jiya Juma’a 10 ga watan Nuwamba a Abuja bayan Luggerewo ya sha kaye a kotun zabe a watan Satumba.

Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan zaben kakakin majalisar APC
Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan zaben kakakin Majalisa. Hoto: Abubakar Luggerewo/ Facebook.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke?

Luggerewo wanda dan jam’iyyar APC ce mai mulki a jihar na wakiltar mazabar Akko ta Tsakiya a Majalisar jihar, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan PDP, ta bayyana mai nasara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin hukuncin, Mai Shari’a, Uzoamaka Ifeyinwa ya tabbatar da nasarar da Luggerewo ya samu a zaben da aka gudanar a watan Maris.

Lauyan mai kara, Barista Caleb Ubale ya ce umarnin kotun kararrakin zabe na sake yin zabe a wasu mazabu a yankin akwai kura-kurai.

Wane hukunci korun zabe ta yi a baya?

Kotun ta amince da korafin Caleb inda ta ce wadanda ake kara ba su kawo kwararan hujjoji da za su gamsar da ita ba, First News ta tattaro.

A watan Satumba kotun kararrakin zabe ta kwace kujerar Luggerewo na jam’iyyar APC tare da umartan sake zabe a wasu mazabu.

Kotun har ila yau, ta ayyana Bashir Gaddafi na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel