Jerin Abubuwa 2 Muhimmai da Ya Kamata Ku Sani Yayin da Ake Yanke Hukuncin Shari’ar Zaben Nasarawa

Jerin Abubuwa 2 Muhimmai da Ya Kamata Ku Sani Yayin da Ake Yanke Hukuncin Shari’ar Zaben Nasarawa

Kotun daukaka kara da ke Abuja za ta yanke hukuncin shari’ar zaben gwamnan jihar Nasarawa a yau Alhamis 23 ga watan Nuwamba bayan tabbatar da David Ombugadu na jam'iyyar PDP.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

A ranar 2 ga watan Oktoba kotun zabe ta kwace kujerar Gwamna Sule Abdullahi na jihar Nasarawa a matsayin gwamnan jihar, Legit ta tattaro.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da shari'ar zaben jihar Nasarawa
A yau ake yanke hukuncin shari'ar zaben jihar Nasarawa. Hoto: Abdullahi Sule, David Ombugadu.
Asali: Twitter

Kotun har ila yau, ta tabbatar da nasarar dan takarar jam’iyyar PDP, David Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaben.

Daga bisani, Gwamna Sule ya daukaka kara don neman sauya hukuncin karamar kotun da ta rusa zabenshi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan APC, ta bayyana mai nasara

Legit ta jero muku abubuwa da ya kamata ku sani game da shari’ar:

1. ‘Yan sanda sun gargadi magoya bayan PDP, APC kan shari’ar

Yayin da ake shirye-shiryen yanke hukunci kan wannan shari’ar, Rundunar ‘yan sanda ta tura sakon gargadi ga dukkan magoya bayan jam’iyyun.

Akwai alamun cewa dukkan bangarorin na zaman doya da manja yayin da ko wace jam’iyya ke hankoron samun nasara a shari’ar.

Dalilin haka, rundunar ta bukaci mutane da su bi a hankali inda ta ce ta shirya daukar mataki kan duk masu son ta da zaune tsaye, cewar Punch.

2. Magoya bayan PDP sun fara addu’ar kwanaki bakwai

Legit Hausa ta ruwaito cewa magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar sun fara addu’o’in kwanaki bakwai saboda neman taimakon ubangiji.

‘Yan PDP sun yi zargin wasu tsiraru na son kwace musu kujera bayan wahalar da suka sha wurin zaban David Ombugadu na jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Shari'ar zabe: An tsaurara tsaro yayin da ake dakon hukuncin kotu a shari'ar gwamnan APC

Daya daga cikin shugabannin taron, Sulaiman Abdullahi ya bayyana wa manema labarai cewa su na da yakinin samun nasara a wannan shari’ar.

Musulmai da Kirista sun fara addu’ar neman nasara

A wani labarin, dandazon Musulmai da Kirista ne su ka fara addu’o’in kwanaki bakwai don neman taimakon ubangiji a shari’ar jihar Nasarawa.

Dandazon jama’an wadanda magoya bayan jam’iyyar PDP ne sun zargi wasu tsiraru da son kwace kujerar David Ombugadu.

Sun yi addu'ar neman taimakon ubangiji don bai wa dan takarsu nasara a shari'ar da za a yanke a yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel