Jigon PDP, Sule Lamido Ya Fallasa Wadanda Su Ka Jefa Najeriya Cikin Wahalar Rayuwa

Jigon PDP, Sule Lamido Ya Fallasa Wadanda Su Ka Jefa Najeriya Cikin Wahalar Rayuwa

  • Babu wanda ya kai talaka halin da yake ciki a yau irin shi karan kan shi a cewar tsohon Gwamna Sule Lamido
  • ‘Dan siyasar ya ce PDP tana kan mulki amma mutane su ka yi waje da ita, su ka gayyato jam’iyyar APC a 2015
  • Duk tsadar rayuwar da ake yi, Sule wanda ya yi mulki a jihar Jigawa ya ce talaka yana girban irin da ya shuka ne

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Jigawa - Da aka yi wata doguwar hira da Sule Lamido, tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya zargi talaka da dauko ruwan dafa kan shi.

Alhaji Sule Lamido ya fadawa Daily Trust cewa PDP tana kan mulki na shekaru 16, amma mutane su ka zabi APC ta karbi ragamar kasar.

Kara karanta wannan

APC ta mayarwa Sule Lamido martani: Har yanzu kura-kuren PDP muke gyarawa

Sule Lamido
Alhaji Sule Lamido Hoto: Mustafa Sule Lamido
Asali: Facebook

Tsige PDP a zaben 2015

Sule yake cewa lokacin da PDP ta yi mulki, an shawo kan tattalin arziki, yafe bashin da ke kan Najeriya kuma an dawo da mutuncin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwararren ‘dan siyasar yana ganin fatali da su da aka yi daga kan mulki saboda Boko Haram, shi ya jefa al’umma a halin da ake ciki har gobe.

Sule ya ce talaka ya jawowa kan shi

Idan wani zai yi magana kan matsin lambar da ake fuskanta a yau, Sule ya ce talaka ne wanda ya yi watsi da Goodluck Jonathan, ya rungumi APC.

"Saboda me zan yi martani? A kan mene? Mu na kan mulki, aka sauke mu...yanzu ku na cewa in yi magana kan wahalar da ake ciki?
Meyasa za ka tambaye ni? Ka tambayi wadanda su ka zabo APC, aka dauko Waliyyi Buhari.

Kara karanta wannan

Ban san yadda yarona ya samu takara ba, sai dai na gani a Facebook – Sule Lamido

Ku tambayi malaman da su ka kawo Muhammadu Buhari da wadanda su ka kawo Emilokan (Bola Tinubu), meyasa za a tambaye ni?

- Sule Lamido

Jigon na PDP wanda ya yaki Bola Tinubu a zaben shugaban kasa, ya ce ba zai yi magana a game da tsarin tallafin fetur ba sai lokacin kamfe.

A yanzu, (APC) su na aiwatar da abubuwan da su ka yi maku alkawari – wahala, azaba da rashin tsaro. Ba ku cikin aminci.
Kun zama talakawa, albashinku a wata ba zai iya sayen buhun shinkafa ba, kuna girban abubuwan da ku ka shuka ne.

- Sule Lamido

Shari'o'in zabe a mulkin APC

Ana da labari Gwamnan jihar Nasarawa ya yi kus-kus da Abdullahi Umar Ganduje awanni bayan APC ta yi galaba kan PDP a shari’ar zabe.

Zuwa yanzu APC ta yi nasara a Kano, Nasarawa, Zamfara da Filato a shario’in zabe, gaba daya jihohin da aka karbe na ‘yan hamayya ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng