Dattawa, Tsohon Shugaban Lauyoyi Sun Soki Tafka da Warwaran Alkalai a Shari’ar Kano

Dattawa, Tsohon Shugaban Lauyoyi Sun Soki Tafka da Warwaran Alkalai a Shari’ar Kano

  • Olumide Akpata ya shiga cikin wadanda su ka yi magana a kan hukuncin zaben gwamnonin jihohi na 2023 a kotu
  • Tsohon shugaban na NBA ya na ganin ya kamata kotun daukaka kara ta yi karin haske a kan hukuncin zaben Kano
  • Shugaban kungiyar NEF ta dattawan Arewa, Ango Abdullahi ya tunawa kotu cewa dole a tabbatar da adalci da gaskiya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Tsohon shugaban kungiyar lauyoyi na kasa (NBA), Olumide Akpata, ya bukaci kotun daukaka kara tayi wa duniya karin bayani.

Tashar Channels ta ce Olumide Akpata ya yi wannan kira ne zuwa ga shugaban babban kotun na kasa, Monica Bolna’an Dongban-Mensem.

Lauyan ya ce akwai bukatar Mai shari’a Monica Bolna’an Dongban-Mensem tayi karin haske ganin abin kunyan da su ka faru a kotunta.

Kara karanta wannan

Shari’ar Kano: Gwamna Abba ba zai maida takardun hukuncin kotu ba Inji Lauyan NNPP

Kotu.
'Yan sanda a waje yayin da Alkalai ke shari'a a Kotu: Getty Images/AFP/PIUS UTOMI EKPEI
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olumide Akpata ya ja hankalin Alkalan kotu

A makon jiya ne alkalan kotun daukaka kara da ke zama a garin Abuja su ka fitar da takardun hukuncin zaben Kano da ya jawo rudani sosai.

Abin da yake cikin takardun na CTC ya sha bam-bam da asalin hukuncin da aka zartar, Olumide Akpata ya ce kyau a fito ayi bayani sosai.

Lauyan ya yi wannan kira ne a shafinsa na Facebook, ya na cewa abin da ya faru ya sake nuna kalubalen da ake fuskanta a kotunan kasar.

"A matsayin shugabar kotun daukaka kara, ya na da muhimmanci Mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ta yi fayyataccen bayani mai gamswar a kan abin kunyar nan.
Wannan zai taimaka wajen shawo kan surutai da korafin ‘Yan Najeriya da mutanen duniya."

- Barista Olumide Akpata

Kara karanta wannan

Kuskuren Cikin Takardun Hukuncin Kano Ba Tuntuben Alkalami ba ne - Farfesa Odinkalu

Manyan Arewa sun yi kira ga Alkalai

Ana haka sai Daily Trust ta rahoto kungiyar dattawan Arewa ta NEF, ta na cewa akwai bukatar kotu ta I a hankali wajen yanke hukunci.

Shugaban NEF, Farfesa Ango Abdullahi ya yi jawabi a Abuja, ya tunawa alkalai aikinsu na kare damukaradiyya da hakkokin al’umma a kasa.

Kamar yadda aka ja hankalin shugaba Bola Tinubu, Ango Abdullahi ya nuna idan alkalai su ka saki layin gaskiya, lallai kasa ta shiga matsala.

Alkalin da ya tsige Gwamnan Kano

Kwanaki aka ji labari Farfesa Chidi Odinakalu yana ta cigaba da bankado bayanai game da tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf da aka yi a kotu.

Cikin Alkalan da su ka tsige Gwamnan Kano akwai yaron Alkalin Alkalai. Shari’ar zaben Gwamnan Kano ta jawo surutu a gida da wajen jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel