Lauyoyin arewa sun kafa sabuwar NBA, sun tsame kansu daga tsohuwar
Wasu lauyoyi sun kafa sabuwar kungiyar lauyoyin Najeriya da manufar kare hakkin su wanda sashi na 40 na kundin tsarin mulkin kasa ya basu.
A wata takarda da Batista Nuhu Ibrahim Esq da Abdulbasit Suleiman Esq suka saka hannu kuma suka mika ga manema labarai, sun ce lamarin ya matukar taba duk wani lauya ballantana na yankin arewacin kasar nan.
"Abinda ke faruwa a cikin kwanakin nan ya bayyana gazawar kungiyar lauyoyin Najeriya na yadda bata iya hada kan jama'a masu banbanci da ke karkashin kungiyar tare da kare dukkan hakkokinsu.
DUBA WANNAN: Batanci ga Annabi: A shirye na ke in rattaba hannu kan hukuncin kisa da kotu ta yanke - Ganduje
"Karfin mahukutanta ya koma na kabilanci da goyon bayan yanki. A matsayin kungiyar wacce ta samu horarwa wurin tabbatar da ci gaba tare da kare hakkin jama'a da 'yancinsu, ya kamata NBA ta kafu fiye da duban yanki ko kabilanci.
"A don haka, ba za mu zuba ido mu ga kungiyar lauyoyin tana kin kare hakkin mambobinta tare da 'yancinsu. Ya kamata a ganta tana aikata abinda take kira a kan shi.
"Kamar yadda bahaushe ke cewa: 'Idan Kura tana maganin zawo, ta yi wa kanta'. Sabuwar kungiyar lauyoyin tana kallon ayyukan NBA tuntuni. Kungiya ce da kowa yake fatan shiganta kafin ya kai matsayin."
Ya bayyana cewa, 'yan sabuwar kungiyar lauyoyin tuni suka fara tuntubar manyan lauyoyin arewacin Najeriya domin saka ranar da za a rantsar da sabuwar kungiyar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng