Tinubu ya yi umurnin nada mataimakin Akeredolu a matsayin mukaddashin gwamna? Gaskiya ta bayyana

Tinubu ya yi umurnin nada mataimakin Akeredolu a matsayin mukaddashin gwamna? Gaskiya ta bayyana

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya magantu kan rahoton cewa watakila ya yi umurnin rantsar da Lucky Aiyedatiwa, mataimakin gwamnan jihar Ondo, a matsayin mukaddashin gwamna
  • Shugaban kasar ya yi karin hasken ne kwana daya bayan ganawarsa da mataimakin gwamnan, yan majalisa da sauran masu ruwa da tsaki kan lamarin
  • Jihar Ondo ta dade tana fama da rikicin siyasa saboda rashin Gwamna Akeredolu a gari sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana hukuncinsa kan rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar Ondo saboda rashin kasancewar Gwamna Rotimi Akeredolu a gari sakamon rashin lafiyar da yake fama da ita.

A cikin wata sanarwa daga ofishinsa a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, Shugaban kasa Tinubu ya ayyana cewa Akeredolu da ke jinya shi ne dai gwamnan jihar ta Kudu maso Yamma, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da matarsa sun yi bikin cika shekaru 34 da aure

Tinubu ya ce har gobe Akeredolu ne gwamnan jihar Ondo
Tinubu ya yi umurnin nada mataimakin Akeredolu a matsayin mukaddashin gwamna? Gaskiya ta bayyana Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Rotimi Akeredolu Aketi
Asali: Twitter

Tinubu ya tsoma baki a rikicin siyasar Ondo

Rikicin da aka dade ana yi ya kasance tsakanin masu biyayya ga Gwamna Akeredolu da mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, amma a yammacin ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba, Tinubu ya gana da bangarorin da shugabannin APC na jihar a fadar shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan ganawarsu, Tinubu, wanda ya magantu ta bakin mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin labarai, Ajuri Ngelale, ya bayyana cewa har gobe Akeredolu ne gwamnan jihar.

Fadar shugaban kasar ta yi karin hasken ne yayin da ake yada rahoton cewa watakila Tinubu ya umurci yan majalisar da su ayyana Aiyedatiwa a matsayin mukaddashin gwamna idan akwai bukatar yin hakan.

Mataimakin Akeredolu da yan majalisa sun yarda da zaman lafiya bayan Tinubu ya tsoma baki

A taron na ranar Juma'a, mataimakin gwamnan, yan majalisa da masu ruwa da tsaki sun yarda da yin sulhu da hada kan gidan bayan shafe tsawon awanni shida ana tattaunawa tsakinsu da shugaban kasa a fadar Villa.

Kara karanta wannan

To fa: Manyan jiga-jigai sun matsa a sauke gwamnan APC a ɗora mataimakinsa a matsayin gwamna

Yayin da yake tabbatar da Akeredolu a matsayin gwamna, shugaban kasar ya yi kira ga kowani bangare da ya rungumi zaman lafiya.

Jawabin na cewa:

"Wannan na nufin cewa Gwamna Akeredolu na nan a matsayin mai girma gwamnan jihar, Aiyedatiwa na nan a matsayin mataimakin gwamna, sannan yan majalisar zartaswa na Jiha sun ci gaba da gudanar da ayyukansu, duk da cewa shugabancin majalisar dokokin jihar da na Jam’iyyar APC a Jihar Ondo basu ce komai ba."

APC ta magantu kan jinyar Akeredolu

A wani labarin, mun ji a baya cewa jam’iyyar APC reshen jihar Ondo ta mayar da martani kan zargin da ake yi na Gwamna Rotimi Akeredolu da ke fama da rashin lafiya ya kashe N7.3bn a tsakanin watannin Yuli da Satumba 2023 ba tare da amincewar majalisar dokokin jihar ba.

Jaridar SaharaReporters, ta yi wannan zargin a cikin rahotonta, inda ta bayyana cewa Akeredolu ya amince da kuɗin ne a lokacin da yake hutun jinya a Jamus na tsawon watanni uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng