Shugaba Tinubu Ya Shiga Tsakani Yayin da Yan Majalisa Suka Fara Shirin Tsige Gwamnan APC

Shugaba Tinubu Ya Shiga Tsakani Yayin da Yan Majalisa Suka Fara Shirin Tsige Gwamnan APC

  • Bola Ahmed Tinubu ya shirya zama da mambobin majasar dokokin jihar Ondo ranar Jumu'a kan rikicin gwamna da mataimakinsa
  • Wata majiya ta ce kafin wannan gayyata ta Tinubu, yan majalisun sun tsara zama da nufin sauke Gwamna Akeredolu su ɗora Aiyedatiwa
  • Shugaban majalisar ya tabbatar da batun ganawar su da shugaban ƙasa da yammacin ranar Jumu'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga tsakani da nufin sasanta rikicin Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo da mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

A rahoton jaridar The Nation, wata majiya ta bayyana cewa shugaba Tinubu ya kira mambobin majalisar dokokin jihar Ondo domin su tattauna ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Yan majalisar dokoki sun shirya zama, zasu ɗora mataimaki a matsayin gwamnan jihar APC

Shugaba Tinubu ya shiga tsakani a rikicin siyasar jihar Ondo.
Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Tsoma Baki Kan Rigimar da Ta Barke Tsakanin Gwamna da Mataimaki Hoto: Oluwarotimi Akeredolu, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A makon da muke ciki ne manyan dattawa da sarakunan gargajiya suka roƙi shugaba Tinubu da ya sa baki a rikicin siyasar domin kaucewa barkewar yamutsi, This Day ra rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba Gwamna Akeredolu da mataimakinsa ba su ga maciji, lamarin da ta kai ga majalisa ta fara yunkurin tsige mataimakin gwamnan.

An tattaro cewa a halin da ake ciki majalisar dokokin ta rabu gida biyu, inda yan majalisa 11 daga cikinsu suka koma bayan mataimakin gwamna, Aiyedatiwa.

Majalisa ta fara shirin sauke gwamnan Ondo

Wasu majiyoyi sun ce yan majalisun 11 sun fara tuntubar wasu ƙusoshi a wajen jihar Ondo kuma an ce su ne suka matsa lamba majalisa ta shirya zama yau Jumu'a.

Ɗaya daga ciki wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya ce zaman na ɗaya daga cikin tsare-tsaren da suka yi a Abuja tare da ƴan majalisa 11 da ke goyon bayan Aiyedatiwa.

Kara karanta wannan

Mataimakin Sanusi a bankin CBN ya fito ya soki hukuncin zaben gwamnan jihar Kano

Ya ce zaman wani shiri ne na ayyana Gwamna Akeredolu a matsayin wanda ba zai iya shugabanci ba tare da bayyana Aiyedatiwa a matsayin gwamnan jihar Ondo.

Wane mataki shugaba Tinubu ya ɗauka kan lamarin?

Shugaban majalisar dokokin Ondo, Oladiji Olamide, ya tabbatar da batun ganawa da shugaba Tinubu, inda ya ce abinda suka tattauna ne zai nuna matakin da za su ɗauka na gaba.

Oladiji ya ce majalisa ta kira zama ranar Jumu'a ne domin ayyana Aiyedatiwa a matsayin muƙaddashin gwamna ba wai tsige Gwamna Akeredolu da sunan ya gaza ba.

Ya ce taron da za su yi da shugaban ƙasa zai gudana ne ranar Jumu'a, 24 ga watan Nuwamba da yamma

“Zamu zauna ne domin bayyana Aiyedatiwa a matsayin mukaddashin gwamna. Har yanzu Gwamnan yana nan a raye,” inji shi.

Shettima ya jagoranci taron NEC a Villa

A wani rahoton na daban Sanata Kashim Shettima da gwamnonin jihohin Najeriya na PDP, APC da LP sun shiga taron NEC a fadar shugaban kasa.

Mataimakin shugaban ƙasar na jagorantar taron NEC karo na huɗu tun bayan rantsar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel