Ganduje Ya Kinkimo Babban Aiki a APC, Ya Fara Shirin Kwace Wata Jiha 1 Daga Hannun PDP

Ganduje Ya Kinkimo Babban Aiki a APC, Ya Fara Shirin Kwace Wata Jiha 1 Daga Hannun PDP

  • Jam'iyyar APC karkashin Abdullahi Ganduje ta rantsar da sabon kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar reshen jihar Ribas
  • Ganduje ya ce wannan kwamitin zai maida hankali wajen jawo mambobin APC da suka sauya sheƙa su dawo gida kuma zai shirya taruka
  • A ranar Laraba bayan kammala taron NWC, kakakin APC ya sanar da korar tsoffin shugabanni na jihar tare da naɗa kwamitin riko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC ta ƙasa ya rantsar da mambobin kwamitin riƙon karya wanda zai riƙe jam'iyyar na wani lokaci a jihar Ribas.

Bikin rantsar da kwamitin ya gudana ne a hedkwatar APC ta ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 12:30 na ranar Jumu'a, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

To fa: Manyan jiga-jigai sun matsa a sauke gwamnan APC a ɗora mataimakinsa a matsayin gwamna

Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje.
Jam'iyyar APC ta rantsar da kwamitin rikon kwarya na jihar Ribas Hoto: OfficialAPCNigeria
Asali: Twitter

Taron ya samu halartar shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, mataimakin shugaban jam'iyya na kudu maso kudu, Victor Giadom da mambobin NWC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta kori shugabanninta na Ribas

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan kwamitin NWC na APC karƙashin Ganduje ya tsige tsoffin shugabannin jam'iyya na jihar Ribas.

Bayan haka kuma aka naɗa sabon kwamitin riko wadda zai jagoranci harkokin APC a jihar tare da shirya tarukan zaben shugabanni a Ribas.

Sakataren watsa labaran APC na ƙasa, Felix Morka, ne ya sanar da korar tsoffin shugabannin ranar Laraba da ta gabata.

Mista Morka ya ce kwamitin gudanarwa (NWC) na APC ta ƙasa ya naɗa Chief Tony Okocha a matsayin shugaban kwamitin riko da Eric Nwibani a matsayin Sakatare.

Sauran mambobin kwamitin mai mutum bakwai su ne, Chibuike Ikenga, Stephen Abolo, Silvester Vidin, Senibo Karibi Dan-Jumbo, da kuma Mis Darling Amadi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da Ganduje da gwamnoni uku, ya musu nasihar yadda zasu ɗauki talakawa

Ganduje ya yi magana a wurin rantsar da kwamitin rikon

Da yake jawabi bayan rantsar da su, Ganduje ya bukaci su shirya kansu domin gudanar da aiki mai wahala na sasanta bangarorin jam'iyya da kuma dawo da waɗanda suka sauya sheƙa.

A ruwayar Premium Times, Ganduje ya ce:

"Ina taya murna ga sabbin mambobin kwamitin riko da aka rantsar. Na tabbata kuna sane da cewa tun 2015 APC ke fama da koma baya ta fuskar rigingimu da kararraki wanda a karshe ya jawo rugujewarta a jihar Ribas."
“Saboda haka, wannan sabon kwamitin NWC ya yi nazari kan al’amura a matakin kasa da kuma daidaikun jama’a kuma ya yanke shawarar yin garambawul."
"Zamu jawo yan uwanmu mu lallashe su, kuma zamu ja hankalin mambobin jam'iyyun siyasa su shigo cikinmu domin gina APC wanda kowa zai alfahari da ita."

Shugaba Tinubu ya yi sabbin naɗe-naɗe a NCS

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya naɗa karin mambobin majalisar gudanarwa a hukumar kwastam ta ƙasa (NCS) ranar Jumu'a.

Waɗanda shugaban ƙasar ya naɗa zasu wakilci kamfanoni masu zaman kansu na tsawon zango ɗaya watau shekaru huɗu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel