Jerin Gwamnonin da Suka Yi Nasara a Kotun Daukaka Kara Kawo Yanzu

Jerin Gwamnonin da Suka Yi Nasara a Kotun Daukaka Kara Kawo Yanzu

Bayan kammala zaben 2023 a Najeriya, mun ga yadda 'yan siyasa da dama suke shige da fice a kotuna domin kare kai ko daukaka karar zaben da aka yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wata al'ada ce a siyasar Najeriya bayan kammala kowanne zabe, za a samu yawan kararraki tun aga kotunan zabe zuwa Kotun Koli, saboda shari'ar zabe.

Babajide Sanwo-Olu/Inuwa Yahaya/Peter Mbah/Abdullahi Sule/Bassey Otu/Legas/Gombe/Enugu/Nasarawa/Cross River/APC/PDP/Kotun Daukaka Kara
Ya zuwa yanzu dai ga jerin gwamnonin da suka samu nasara a Kotun Daukaka Kara Hoto: Babajide Sanwo-Olu, Abdullahi Sule, Peter Mbah
Asali: Twitter

A yanzu dai an gama da shari'o'i na kotunan zaben gwamnoni, wasu na Kotun Daukaka Kara wasu kuma sun nufi Kotun Koli, Legit ta ruwaito.

Yayin da Kotun Daukaka Karar ta kori wasu gwamnoni, wasu kuma sun samu nasara. A kasa mun jero gwamnonin da suka samu nasara a Kotun Daukaka Kara.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara da sanya ranar yanke hukuncin shari'ar zaben gwamnan Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babajide Sanwo-Olu

Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a jihar Legas ta tabbatar da gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu da mataimakinsa Obafemi Hamzat a matsayin wadanda suka lashe zaben gwamnan jihar da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

Kotun ta kori karar da ‘yan takarar jam’iyyar PDP, Abdulazeez Adediran da takwaransa na jam’iyyar Labour, Gbadebo Rhodes-Vivour suka shigar kan rashin hujjoji.

Inuwa Yahaya

Yahaya, gwamnan Gombe kuma dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar da ya gabata ya samu nasara a Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja.

Muhammad Barde, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben, ya shigar da kara a gaban kotu, yana mai jaddada cewa tazarcen Yahaya bai yi daidai da tanadin dokar zabe ba.

Abdullahi Sule

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, na daya daga cikin gwamnonin da Kotun Daukaka Kara ta yi wa rana bayan da ta yi watsi da hukuncin korar sa da kotun kararrakin zabe ta yi daga gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Bayan shari'ar Nasarawa, kotu ta sake yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan APC, ta ba da dalili

A baya dai kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Nasarawa ta kori gwamnan tare da bayyana David Ombugadu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zabe.

Sai dai Kotun Daukaka Kara ta soke hukuncin da karamar kotun ta yanke a hukuncin da ta yanke a ranar Alhamis 23 ga watan Nuwamba.

Peter Mbah

Har ila yau, bangaren kotun daukaka kara na Legas ya tabbatar da nasarar Peter Mbah, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Enugu da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris.

Kotun ta yi watsi da karar da Chijioke Edeoga na jam’iyyar Labour ya shigar a zaben kan rashin cancanta.

Kotun ta bayyana cewa jam’iyyar Labour da Edeoga ba su gabatar da wata kwakkwarar shaida da ke nuna cewa takardar bautar kasa (NYSC) ta gwamnan ta jabu ce ba.

Bassey Otu

Sashen Kotun Daukaka Kara na Legas ya kuma tabbatar da nasarar Gwamna Otu na Jihar Kuros Ribas a zaben Gwamnan Jihar da ke Kudu-maso-Kudancin kasar da aka yi a ranar 18 ga Maris.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Kano: Kotun Koli za ta warware rudanin da aka samu a Kotun Daukaka Kara, NNPP

Kamar Mbah, Kotu ta yi watsi da daukaka karar Farfesa Sandy Onor na jam’iyyar PDP saboda rashin cancanta.

Bala Mohammed

Ita ma bangaren kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da nasarar da gwamnan PDP, Bala Mohammed ya samu a karar zaben gwamnan jihar Bauchi.

A hukuncin daya yanke, kwamitin mutane uku na kotun daukaka kara ya yi watsi da karar da jam’iyyar APC da dan takararta a zaben, Sadique Abubakar suka shigar.

Kungiyar Izala ta gayyaci Dr. Idris Abdul'aziz zaman mukabala

Har ila yau, daga jihar Bauchi, jiya muka kawo maku labarin, wata takardar gayyata da kungiyar Izala Jos ta aike wa Dr. Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi, Bauchi, na zaman mukabala.

Kungiyar na son Dr. Abdul'aziz ya yi zaman mukabala da Sheikh Kantana a dakin taro na Multi-purpose dake Bauchi, don tattauna wa kan wasu kalamai da malamin ya yi a majalisinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.