Shari’ar Gwamna: Cikin Yarbawa Ya Tsure Yayin da Zanga Zanga Ya Barke a Kano
- Wata kungiyar Yarbawan da ke rayuwa a garin Kano tayi magana game da yanayin siyasar da ake ciki a yanzu
- Shugabannin kungiyar sun fara tsorata ganin zanga-zanga sun barke a dalilin tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf a kotu
- A cewar Taofeek Olaosebikan, wasu za sui ya kai wa Yarbawa hari a Kano saboda kurum Bola Ahmed Tinubu bayarabe ne
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Kungiyar wasu Yarbawa da ke zama a garin Kano sun nuna damuwarsu a kan abubuwan da ke faruwa bayan rusa zaben Gwamna.
A rahoton Punch na ranar Alhamis, an fahimci cewa kungiyar Yarbawan Kano ta ankarar cewa tana tsoron za a iya kai mata hari a halin yanzu.
Yarbawa sun fara dar-dar a garin Kano
Fargabar da kungiyar ta ke yi shi ne tsoron a auka masu saboda Bola Ahmed Tinubu yake rike da mulki yayin da aka tsige gwamnan jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan kungiya ta Yarbawa mazauna jihar Kano ta ce ta na bibiyar abubuwan da ke faruwa a shari’ar Abba Kabir Yusuf da kuma APC a kotu.
Sakatare Janar na kungiyar, Taofeek Olaosebikan ya shaidawa manema labarai cewa suna kira ga shugabannin Yarbawa su zauna da Bola Tinubu.
Babban abin da Yarabawan Kano ke tsoro
A taron manema labaran da ya kira, Taofeek Olaosebikan ya ce abin zai iya shafar su saboda Mai girma shugaban Najeriya bayarabe ne irinsu.
A faifen bidiyon da Legit ta ci karo da shi a Facebook, an ji Olaosebikan yana cewa akwai masu tunanin wasu sun yi katsalandan a shari’ar Kano.
Kano: Ana so shugabanni su hadu da Tinubu
Kungiyar ta bukaci manya da sarakunan Yarbawa kamar su Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II da Shugaba Olusegun Obasanjo su sa baki.
Vanguard ta ce Yarbawan sun bukaci Oba na Legas, Alaken Agba, Awujare na kasar Ijebu da Olubadan na Ibadan su gaggauta zama da Tinubu.
Olaosebikan da kungiyarsa suna ganin wasu za su iya fusata, su zargi shugaban kasa da hannu wajen tsige Abba Kabir Yusuf da aka yi a kotu.
A karshe za a iya huce takaicin a kan Yarbawan da ke Kano saboda Tinubu bayarabe ne.
Hukuncin kotu ya jawo rudani a Kano
A farkon makon nan an ji labarin yadda hukuncin zaben Gwamnan Kano yake neman tada zaune tsaye saboda tsige Abba Kabir Yusuf.
Takardun CCT sun jawo rudani wanda wasu su ke ganin hakan ya sake bata darajar Alkalai da kotuna da wasu ke zargi da rashin yin adalci.
Asali: Legit.ng