Musulmai da Kirista Sun Fara Addu’o’in Kwanaki 7 Don Neman Taimakon Allah a Shariar Gwamnan APC

Musulmai da Kirista Sun Fara Addu’o’in Kwanaki 7 Don Neman Taimakon Allah a Shariar Gwamnan APC

  • Wasu mazauna Lafia a jihar Nasarawa sun fara addu’ar kwanaki bakwai don neman yardar ubangiji a shari’ar zaben gwamnan jihar
  • Masu addu’ar da su ka hada da Musulmai da Kirista sun fito addu’ar ce a yau Litinin 20 ga watan Nuwamba
  • Sun yi addu’ar neman ikon ubangiji na bai wa David Ombugadu na jam’iyar PDP nasara a shariar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Nasarawa – Yayin ake shirye-shiryen yanke hukuncin shari’ar zaben gwamnan a jihar Nasarawa, ‘yan jihar sun fara addu’ar samun nasara.

‘Yan jihar da su ka hada da Musulmai da Kirista sun fara addu’ar ce ta kwanaki bakwai don neman samun nasarar jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Jama'a sun hada-kai, sun yi karar Bola Tinubu a kotu kan nade-naden shugabannin INEC

'Yan jihar Nasarawa sun fara aduu'o'in kwanaki 7 don neman yardar Allah a shari'ar zabe
Kotun daukaka kara ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben jihar Nasarawa. Hoto: D. Ombugadu, Abdullahi Sule.
Asali: Facebook

Mene bukatar mazauna Nasarawa?

Mazauna jihar sun bayyana cewa sun fara wannan addu’ar ce don tabbatar da nasarar David Ombugadu na jam’iyyar PDP nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fara wannan addu’a ce a yau Litinin 20 ga watan Nuwamba inda su ke bukatar yin hukunci na adalci don bai wa wanda su ka zaba nasara a shari’ar.

Wani mazaunin jihar, Ustars Sulaiman Abdullahi ya ce Allah ya na sauraran komai wanda shi ne mahaliccin duniya.

Ya ce sun a rokon Allah ya ba su abin da su ka zaba a zaben ba wadanda wasu ke son kakaba musu karfi da yaji ba, Vanguard ta tattaro.

Mene bukatar mutanen Nasarawa?

A cewarsa:

“Mun zabi dan jam’iyyar PDP da dan takararta a ranar 18 ga watan Maris saboda samun sauyi a wannan jihar.
“Amma wasu na son su hana mu abin da mu ka zaba karfi da yaji. Za mu ci gaba da addu’a don neman adalci a wurin ubangiji.”

Kara karanta wannan

Shari’ar gwamnan Kano: Yan APC sun fara azumin neman nasara yayin da Abba ya garzaya Kotun Koli

A bangaren shi, Rabaran Emmanuel Bako ya ce za su ci gaba da neman taimakon ubangiji inda ya ce ubangiji ba ya bacci, Chronicles ta tattaro.

Ya ce:

“Ubangijinmu ba ya bacci, zai bai wa wadanda ke son kwace mulki kunya, su na son kwace nasarar David Ombugado na PDP.”

Kotun daukaka kara ta tanadi hukuncin zaben Nasarawa

Kun ji cewa, kotun daukaka kara ta tanadi hukuncin shari’ar zaben jihar Nasarawa da ake ci gaba da yi.

Wannan na zuwa ne bayan kotun zabe ta rusa nasarar Gwamna Sule na APC tare da bai wa David Ombugadu na jam’iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel