Kujera Za Ta Jawo Sabuwar Rigima Tsakanin Wike da Gwamnoni a Jam’iyyar PDP

Kujera Za Ta Jawo Sabuwar Rigima Tsakanin Wike da Gwamnoni a Jam’iyyar PDP

  • Akwai masu ganin ya kamata Samuel Anyanwu ya sauka daga kujerar Sakatare tun da ya tafi takarar Gwamna a jihar Imo
  • Tsohon Sanatan na Imo ta yamma ya ki hakura da mukaminsa, ya yi kutun-kutun wajen hana Sunday Udeh Okoye ya gaje shi
  • BOT da Gwamnoni sun bukaci ayi biyayya ga umarnin kotu a nada sabon Sakatare, Nyesom Wike ya taka masu burki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Sabani ya bijiro tsakanin gwamnonin jihohin PDP da jagora a jam’iyyar, Nyesom Wike wanda shi ne ministan harkokin Abuja.

Jaridar This Day ta ce Abin da ya jawo rikicin shi ne kokarin dawo da Sanata Samuel Anyanwu a matsayin Sakataren jam’iyyar PDP na kasa.

Kara karanta wannan

Tsohon Sanatan APC Ya Yi Allah Wadai da Kotu a Kan Tsige Gwamnonin PDP da NNPP

Anyanwu ya yi takarar gwamna a jihar Imo, amma Hope Uzodinma ya yi galaba a kan shi.

Jam’iyyar PDP
Jagororin Jam’iyyar PDP Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Samuel Anyanwu ya ki barin PDP-NWC

Kafin a shiga zaben gwamnan, an bukaci ‘dan siyasan ya sauka daga kan kujerar da yake kai a NWC, ya ba wani damar zama sakataren.

Wasu sun bada shawarar tsohon shugaban matasan na PDP na kasa, Sunday Udeh Okoye ya canji Anyanwu, amma dai hakan bai yiwu ba.

Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar adawar ya hana Sunday Udeh Okoye ya gaji kujerar, PDP NWC ta ce ba za a kawo mata sabon fuska ba.

Kotu ta ce PDP ta canza Sanata Anyanwu

Ana haka sai kotun tarayya da ke zama a garin Enugu ta yanke hukunci cewa dole uwar jam’iyya ta nada sabon sakataren PDP na kasa.

Kara karanta wannan

Tsohon jigo ya fadi barazanar da takarar Atiku ta ke fuskanta daga jagororin PDP

Rahoton ya ce Anyanwu ne ya yi gaggawa zuwa Abuja, ya hana a rantsar da Okoye da nufin ya dawo kan kujerar da ya bari kafin zabe.

Amma wasu gwamnonin jihohi sun taka masa burki, su ka hana tsohon sanatan rike matsayinsa a majalisar gudanarwa na jam’iyyar.

Matsayar shugaban PDP

Shugaban PDP na rikon kwarya, Ambasada Illya Damagum ya ce Anyanwu ba zai koma ofis ba domin kotu sun yanke hukunci mabanbanta.

A matsayinsa na shugaban BOT, Adolphus Wabara ya bukaci a nada sabon sakatare, a dalilin haka Nyesom Wike ya caccaki dattawan PDP.

Facakar dukiyar al'umma a jihar APC

Mu na da labari Gwamna Babajide Sanwo Olu ya amince a saye fitilun Naira biliyan 3 da turaren Naira miliyan 7.5 a gidan gwamnatin Legas.

Ana zargin Gwamnatin Legas ta facaka saboda za a kashe miliyoyi a kan abubuwan da ake tunanin ba su da muhimmanci a halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Dalilai 4 da suka sa Anyanwu na PDP ya fadi zaben gwamnan Imo na 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng