Shari’ar Zabe: An Tsaurara Tsaro Yayin da Ake Dakon Hukuncin Kotu a Shari’ar Gwamnan APC

Shari’ar Zabe: An Tsaurara Tsaro Yayin da Ake Dakon Hukuncin Kotu a Shari’ar Gwamnan APC

  • Rundunar ‘yan sanda ta tsaurara tsaro yayin da ake dakon yanke hukuncin shari’ar zaben jihar Nasarawa
  • Rundunar ta ce ta yi hakan ne don dakile duk wani shiri na ta da zaune tsaye kafin da kuma bayan yanke hukuncin
  • Makaddashin kwamishinan ‘yan sanda a jihar, DCP Shettima Muhammad shi ya bayyana haka ga manema labarai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Nasarawa – Yayin da ake shirye-shiryen yanke hukuncin shari’ar zaben jihar Nasarawa, an tsaurara tsaro a lungu da sako na jihar.

Rundunar ‘yan sanda a jihar ta kara yawan jami’an tsaro a duk fadin jihar don tabbatar da tsaro kafin da kuma bayan yanke hukuncin.

An tsaura tsaro yayin da ake shirye-shiryen yanke hukuncin kotun shari'ar gwamnan APC
Shari’ar Zabe: An girka tsaro a jihar Nasarawa. Hoto: Abdullahi Sule, David Ombugadu.
Asali: Facebook

Mene ‘yan sanda ke cewa kan shari’ar Nasarawa?

Kara karanta wannan

Kano: Jigon NNPP ya tona asirin hanyar da APC ke bi don mayar da jihar karkashin ikonta saboda 2027

Mukaddashin kwamishinan ‘yan sanda a jihar, DCP Shettima Muhammad shi ya bayyana haka yayin gana wa da manema labarai a Lafia.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammad ya ce rundunar su ta yi hadaka da sauran jami’an tsaro don samar da tsaro a dukkan lungunan jihar, Tribune ta tattaro.

Ya ce hakan zai dakile duk wani yunkuri na ta da zaune tsaye bayan yanke hukuncin kotun daukaka kara a jihar.

Wane shawara ‘yan sanda su ka bai wa ‘yan siyasa?

Shettima ya shawarci ‘yan siyasa da su ja kunnen magoya bayansu kafin da kuma bayan yanke hukuncin.

Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon yanke hukuncin kotun daukaka kara tsakanin jam’iyyar APC da kuma PDP, cewar Leadership News.

Kotun zabe a kwanakin baya ta rusa zaben Gwamna Sule Abdullahi na jam’iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Shari'ar gwamnan Kano: Jami'an tsaro sun bankado wani shirin tayar da tarzoma, sun gargadi al'umma

Kotun har ila yau, ta tabbatar da nasarar David Ombugadu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.

Daga bisani, Gamna Sule ya daukaka kara zuwa kotu don neman sauya hukuncin karamar kotun.

Musulmai da Kirista sun fara addu’ar nasara a Nasarawa

A wani labarin, magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa sun fara addu’ar kwanaki bakwai don neman nasara a kotu.

Magoya bayan wadanda su ka hada da Musulmai da Kirista sun bayyana cewa wasu na son kwace musu nasara a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.