Abba Ya Kinkimo Manyan Ayyuka Duk da Kotun Daukaka Kara ta Tsige Gwamnatin NNPP

Abba Ya Kinkimo Manyan Ayyuka Duk da Kotun Daukaka Kara ta Tsige Gwamnatin NNPP

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya kira taron ‘ya ‘yan jam’iyyar NNPP bayan dawowarsa Kano a karshen makon da ya wuce
  • Wannan ne zaman farko da aka yi bayan kotun daukaka kara ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf daga kan mulki
  • Gwamnan Kano ya jaddada mubaya’arsa ga Kwankwaso ya kuma ce ba za su fasa yi wa jama’a ayyuka a jihar Kano ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin cigaba da ayyukan da ya sa a gaba duk da rashin nasara a kotu.

Kotun daukaka kara ta tsige Abba Kabir Yusuf, amma a wani bidiyo da hadiminsa ya wallafa a Twitter, ya nuna ba zai karaya ba.

Babban Mai taimakawa Gwamnan a kafofin sadarwa na zamani, Malam Abdullahi Ibrahim ya fitar da bidiyon da safiyar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fayyace ainihin sababin tsige Abba, gwamnan Filato a Kotu

NNPP.
Gwamna Abba da Kwankwaso a taron NNPP a Kano Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Za a fara aikin gadoji da fansho a Kano

A bidiyon, za a iya jin Mai girma gwamnan ya na cewa a makon gobe za su kaddamar da aikin fara gina gadajen sama biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga haka, gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta cigaba da biyan fansho da giratutin ma’aikatan da su ka ritaya daga makon nan.

A cewar Abba Gida Gida, kamar yadda aka yi gadoji hudu a mulkin Rabiu Kwankwaso, gwamnatin NNPP za tayi koyi da jagoranta.

Taron manyan NNPP a jihar Kano

Gwamnan ya yi jawabin nan ne a wani muhimmin taro da jagororin jam’iyyar NNPP na reshen Kano su ka yi a yammacin Lahadin nan.

Legit ta samu labari an yi taron ne a gidan tsohon Gwamna, Rabiu Musa Kwankwaso.

Wadanda su ka samu halarta sun hada da mataimakin gwamna, sakataren gwamnati da ‘yan majalisa irinsu Abdulmumin Jibrin.

Kara karanta wannan

Wasu sun tsinke da lamarin Tinubu da Kotu ta tsige gwamnonin adawa 3 a kwana 4

Abba ya godewa Kwankwaso

A karshe gwamnan ya jaddada biyayyarsa ga Rabiu Kwankwaso, ya fadawa magoya baya cewa sam ba za su karaya da shari’ar kotu ba.

Abba ya ce har gobe suna tare da madugun Kwankwasiyya, kuma sun gwammace su rasa komai a kan su rabu da uban tafiyar siyasarsu.

Meyasa kotu ta tsige Abba Kabir Yusuf?

Dazu aka samu labari Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya nesanta Bola Tinubu da hannu wajen tsige Abba Kabir Yusuf a kotu.

Cif Bayo Onanuga ya ce rashin bin ka’idojin zabe da tsarin mulki shi ne silar soke zaben Gwamnan Kano a babban kotun daukaka kara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng