Tsohon Jigo Ya Fadi Barazanar da Takarar Atiku Ta ke Fuskanta Daga Jagororin PDP
- Umar Ardo ya bayyana cewa duk da Atiku Abubakar ne ya rike tutar PDP a 2019 da 2023, yana da jan aiki gaban shi
- ‘Dan siyasar wanda ya fito daga jihar Adamawa ya nuna Nyesom Wike ya yi karfi a PDP bayan zaben 2015 zuwa yanzu
- Kafin Atiku ya sauya-sheka daga APC zuwa PDP a 2017, Dr. Ardo ya ce Gwamnoni sun yi karfi a jam’iyyar adawar
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Umar Ardo fitaccen ‘dan siyasa ne a Arewacin Najeriya, ya na cikin wadanda aka rika rikici da su a jam’iyyar PDP a shekarun nan.
Punch ta samu lokaci ta yi hira da Dr. Umar Ardo, ta tattauna da shi a kan rikicin PDP, sauya-shekarsa da kuma mulkin Muhammadu Buhari.
A hirar da aka yi da ‘dan siyasar, ya nuna cewa jagororin jam’iyyar PDP ba su tare da Atiku Abubakar duk da ya samu tikitin zaben 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan PDP na goyon bayan Atiku?
"Ba na tunani mafi rinjayen shugabannin jam’iyyar suna tare da Atiku Abubakar har yanzu.
Ka da a manta Atiku ya dawo PDP ne a 2017, bayan ya tafi APC, a lokacin da Nyesom Wike a matsayin gwamna ya na rike da jam’iyyar.
Shi (Wike) ne ya kori Ali Madu Sheriff daga shugaban jam’iyya, kuma shi ne a Fatakwal ya kawo kwamitin rikon kwaryan Ahmad Makarfi."
- Dr. Umar Ardo
Nyesom Wike ya fi Atiku karfi a PDP?
Dr. Ardo yake cewa bayan Wike ya yi sanadiyyar kawo Makarfi sai Uche Secondus ya zama shugaban jam’iyya, Atiku bai san ana yi ba.
Kamar yadda ya fada, gwamnoni suna da karfi a PDP har ta kai sun ba Atiku sharadin sai ya goyi bayan wasu ‘yan takaransu a jihohi.
Tsohon jagoran na PDP ya ce a haka aka kakabawa Atiku Amadu Fintiri a Adamawa, kwanaki aka ji shi ya taya Wike murnar zama Minista.
Yadda Atiku Abubakar ya samu tikitin PDP
"Kun ga rawar da Wike ya taka a tsige Secondus, duk da ya saba doka, aka kawo Ayu.
Atiku ya samu takarar shugaban kasa a 2019 da 2023 ne saboda wasu abubuwa da su ka yi tasiri a wajen siyasar cikin gidan jam’iyyar PDP."
- Dr. Umar Ardo
Atiku yana so a hada-kai kafin 2027
Jam’iyya mai alamar kayan dadi za ta iya kawo cikas wajen haduwar PDP, LP da NNPP kamar yadda labari ya gabata a makon da ya gabata.
Atiku Abubakar ya fara kiran ‘yan adawa su yi wa jam’iyyar APC taron dangi, amma NNPP ta nuna dole a ba Rabiu Kwankwaso tikitin yin takara.
Asali: Legit.ng