"Kada a Kwace Abin Da Mutane Suka Zaba" Shehu Sani Ya Fadawa Kotu Gabanin Hukuncin Kano
- Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi martani kan shirye-shiryen yanke hukuncin zaben gwamna a jihohin Kano da Plateau
- Sani ya ce bai kamata kotun daukaka kara ta kwace kujerun wadannan gwamnoni ba don ceto dimukradiyya a kasar
- Ya ce mutane ne suka zabi wadannan gwamnoni don haka ya kamata a bar musu abin a suka zaba
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilin da ya sa bai kamata kotun daukaka kara ta kwace kujerar Abba Kabir na Kano ba.
Sani ya kuma ce bai kamata kotun ta rusa zaben gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ba saboda ceto dimukradiyya, Legit ta tattaro.
Mene Shehu ke cewa kan Kano, Plateau?
Ya ce barin wadannan gwamnoni shi zai kara daga martabar dimukradiyya wurin samun jam'iyyu daban-daban kan mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan ya bukaci kotun da kada ta ruguza muradun mutane da suka zabi wadannan gwamnoni.
Tsohon sanatan ya bayyana haka a shafin Twitter a yau Laraba 15 ga watan Nuwamba.
Wane shawara Shehu ya bayar kan Kano, Plateau?
"Ya kamata kotun daukaka ta ceto dimukradiyya wurin yin tsarin jam'iyyu daban-daban.
"Bai kamata ta sauya sakamakon zaben jihohin Kano da Plateau ba."
Idan ba ku mantaba a baya kotun zabe ta kwace kujerar Gwamna Abba Kabir na jihar Kano a matsayin gwamnan jihar.
Har ila yau, kotun ta tabbatar Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen zababben gwamna a jihar.
A jihar Plateau, kotun ta tabbatar da Gwamna Caleb Mutfwang na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.
Yayin da ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar APC a jihar, Nentawe Goshwe kan rashin gamsassun hujjoji.
An tsaurara tsaro a Kano
A wani labarin, an baza jami'an tsaro ko ina a cikin jihar Kano saboda shirye-shiryen yanke hukuncin kotun daukaka kara.
A baya, karamar kotun ta kwace kujerar Abba Kabir tare da tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.
Asali: Legit.ng