Zanga-Zanga Ta Ɓarke Bayan Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Yan Majalisar Tarayya 4 Na PDP

Zanga-Zanga Ta Ɓarke Bayan Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Yan Majalisar Tarayya 4 Na PDP

  • Zanga-zanga ta ɓarke a Kotun kolin Najeriya kan hukuncin Kotun ɗaukaka kara na tsige ƴan majalisar tarayya na PDP da suka fito daga Filato
  • Sun miƙa takardar adawa da matakin Kotun ga Alkalin alkalan Najeriya (CJN), mai shari'a Olukayode Ariwoola
  • Shugaban tawagar masu zanga-zangar ya yi zargin cewa akwai hannun wasu jiga-jigan APC a lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Masu zanga-zanga sun mamaye Kotun kolin Najeriya a domin nuna adawarsu da hukuncin tsige mambobin majalisar wakilan tarayya na PDP huɗu daga Filato.

Zanga-zanga a Kotun kolin Najeriya.
Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye Kotun Koli Kan Tsige Yan Majalisar Tarayya 3 na PDP Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Gungun masu zanga-zangar sun yi haka ne bayan Kotun ɗaukaka ƙara ta tsige ƴan majalisar tarayya na PDP daga jihar Filato kan wasu kura-kurai na kafin zaɓe.

Kara karanta wannan

Yajin NLC: Harkoki sun tsaya cak yayin da ma'aikata suka zaɓa wa kansu mafita a babban birnin jihar PDP

Mutane sama da 1,000 ne suka yi zanga-zangar karkashin gamayyar ƙungiyoyi masu fafutukar tabbatar da adalci a Afirka (CJA), kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma sun miƙa takardar ƙorafe-ƙorafen su ga Alkalin alƙalan Najeriya (CJN), Mai shari'a Olukayode Ariwoola, Channels tv ta ruwaito.

A cewar masu zanga-zangar, kotun daukaka kara, bisa hukuncin da ta yanke, ta dakile muradin masu kaɗa kuri'a a jihar Filato lokacin da ta ayyana ‘yan takarar da suka fadi zabe a matsayin wadanda suka lashe kujerun majalisar wakilai.

Da yake jawabi ga ƴan jarida bayan miƙa takarda ga CJN, shugaban ƙungiyar CJA na ƙasa, Dakta Daniel Okwa, ya ce hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara ka iya tada yamutsi a Filato.

'Muna zargin akwai hannun jiga-jigan APC'

Ya ƙara da cewa ƙungiyar ta zo Kotun koli ne domin neman CJN ya tsoma baki kan wannan hukuncin na korar baki ɗaya ƴan majalisar tarayyan PDP da suka fito daga Filato.

Kara karanta wannan

Sylva Vs Diri: Karamar hukuma ɗaya tal da zata raba gardama a zaben Gwamnan Bayelsa ta bayyana

Ya kuma bayyana cewa suna zargin wasu jiga-jigan jam'iyyar APC ne suka kitsa makirci wanda ya sa Kotun ta kori ƴan majalisun daga majalisar wakilan tarayya.

Yajin Aikin NLC Ya Gamu da Babban Cikas a Jihar Ƙaduna

A wani labarin na daban An samu rabuwar kai a jihar Kaduna, wasu ma'aikata sun shiga yajin aiki wasu kuma sun fita wurin aiki kamar yadda suka saba.

A cewar shugaban NLC na jihar, hakan ta faru ne saboda sanarwan ba ta zo musu a kan lokaci ba amma zasu tabbatar da an bi umarni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel