Zaben Bayelsa: Bayan Tattara Sakamakon Kananan Hukumomi, an Fadi Wanda Ke Kan Gaba da Kuri'u Dubu 65

Zaben Bayelsa: Bayan Tattara Sakamakon Kananan Hukumomi, an Fadi Wanda Ke Kan Gaba da Kuri'u Dubu 65

  • Yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zabe, Gwamna Diri na kan gaba a yawan kuri'u
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Diri na jam'iyyar PDP na bai wa Sylva na APC kuri'u fiye da dubu 65
  • Wannan na zuwa bayan ayyana sakamakon zaben karamar hukumar Ijaw ta Kudu a jihar wacce ke da tasiri

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bayelsa - Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya ci gaba da ba da ratar kuri'u masu yawan gaske a zaben jihar.

Diri wanda ke takara a jam'iyyar PDP kuma ya ke neman zarcewa a kan kujerar na ba da ratar kuri'u fiye da dubu 65.

Diri na kan gaba da kuri'u sama da dubu 65 a jihar Bayelsa
An bayyana wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Bayelsa. Hoto: T. Sylva, D. Diri.
Asali: Facebook

Kananan hukumomi nawa aka sanar a Bayelsa?

Kara karanta wannan

"Allah ya ba ku ikon sauke nauyi", Tinubu ya taya Diri, Ododo, Uzodimma murna

Bayan sanar da sakamakon karamar hukumar Ijaw ta Kudu Diri na bai wa Sylva na APC kuri'u dubu 65,088, Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya samu kuri'u dubu 175,196 yayin Sylva na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 110,108, cewar Leadership.

Har ila yau, Hukumar Zabe mai Zaman Kanta, INEC ta sanar da Gwamna Douye Diri a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa karo na biyu.

Gwamna Diri ya lashe zaben gwamna a Bayelsa

Diri ya doke mai bisa wato dan takarar jam'iyyar APC a jihar, Timipre Sylva da kuri'u dubu 175,196.

Wannan na zuwa ne yayin aka kai ruwa rana a zaben da aka kada a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba a jihar Bayelsa.

A ranar Asabar din ce kuma aka gudanar da zabukan jihohi a Imo da Kogi da ke Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: INEC Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Bayelsa

Sylva ya lashe wata karamar hukuma a Bayelsa

A wani labarin, dan takarar jam'iyyar APC, Timipre Sylva ya lashe zaben karamar hukumar Brass a jihar Bayelsa.

Sylva ya doke takwaransa na jam'iyyar PDP kuma gwamnan jihar, Douye Diri a zaben da aka kada a jiya Asabar 11 ga watan Nuwamba.

Wannan na zuwa ne bayan da aka tattara sakamakon zaben dukkan kananan hukumomi inda Diri ke kan gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel