Labari Da Dumi-Dumi: Hukumar INEC Ta Sanar da Duka Wuraren da Aka Soke Zabe a Kogi
- INEC ta tabbatar da cewa an dakatar da shirya zabe a wuraren da aka samu sakamakon bogi suna yawo a kogi
- Kwamishinan Hukumar zaben ya fitar da jawabi cewa ba za a karbi duk wani sakamako da ba daga rumfa ya fito ba
- Muhammad Kudu Haruna ya shaida cewa zuwa yammacin Lahadi za a ji matsayar da INEC ta dauka a zaben jihar
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kogi - Hukumar INEC ta bada sanarwar dakatar da zaben sabon gwamna a wasu daga cikin bangarorin jihar Kogi.
Hukumar gudanar da zabe mai zaman kan ta watau INEC ta fitar da sanarwa a shafin Twitter a yammacin yau Asabar.

Source: Twitter
Sanarwar ta fito ne daga ofishin Kwamishinan yankin Arewa maso tsakiya wanda ya na cikin kwamitin watsa labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhammad Kudu Haruna ya ce hukumar zabe ba za ta karbi sakamakon wuraren da aka samu kuri’un bogi a Kogi ba.
Zaben Kogi: Jawabin Kwamishinan INEC
"Hukumar ta samu rahoton da ya shafi samun malaman zabenmu a jihar Kogi da saba doka, musamman lamarin sakamakon kuri’u kafin a fara dangwala kuri’u.
Rahotanni sun nuna lamarin ya auku ne a kananan hukumomin Adavi, Ajaokuta, Ogori/Magongo, Okehi da Okene.
Idan abin ya fi kamari a Ogori/Magongo ya shafi rumfunan zabe tara a cikin goma.
Ko kadan ba za a yarda da wannan ba. Duk sakamakon da bai fito daga hannun hukuma a rumfunan zabe ba, ba zai samu karbuwa ba."
- Muhammad Kudu Haruna
Sanarwar ta ce a sakamakon haka an dakatar da zaben Gwamnan a mazabu tara da ke karamar hukumar Ogori/Magongo da ke Kogi.
Mazabun nan sun hada da Eni, Okibo, Okesi, Ileteju, Aiyeromi. Ragowar kuma su ne Ugugu, Obinoyin, sai kuma Obatgben da Oturu.

Kara karanta wannan
Zaben jihohi: Abubawa 3 da baku sani ba game da dan takarar jam'iyyar APC a zaben
Muhammad Haruna ya shaida cewa ana binciken abin da ya faru a sauran kananan hukumomi, kuma za a fitar da matsaya nan da sa’o’i 24.
INEC ta sanar da cewa ba za ta bari ayi magudi a zaben da ake gudanarwa a jihar ba. Dama can Dino Melaye ya yi irin wannan kira.
EFCC da DSS wajen zaben Kogi
Dazu an ji labari DSS suna ta sintiri a rumfar zaben da ake tsammanin ‘Dan takaran PDP a zaben watau Dino Melaye zai jefa kuri’arsa.
Haka zalika hukumar EFCC ta aika runduna ta musamman watakila saboda masu sayen kuri’u domin ganin abubuwa sun tafi daidai.
Asali: Legit.ng
