Kotu Ta Yi Fatali da Korafin PDP, Ta Bai Wa LP Nasara a Zaben Majalisar Tarayya a Anambra

Kotu Ta Yi Fatali da Korafin PDP, Ta Bai Wa LP Nasara a Zaben Majalisar Tarayya a Anambra

  • Kotun kararrakin zabe da ke Awka ta jihar Anambra ta tabbatar da nasarar Afam Victor Ogene na jam’iyyar LP
  • Kotun ta kuma yi fatali da karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Chukwuka Onyema ya shigar na kalubalantar zaben
  • Ogene yayin sanar da sakamakon a zaben watan Faburairu ya samu kuri’u 10,851 yayin da Onyema ya samu kuri’u 10,619

Jihar Anambra – Kotun sauraran kararrakin zabe ta majalisar Tarayya ta kori karar dan jam’iyyar PDP, Chukwuka Onyema a mazabar Ogbaru a jihar Anambra.

Kotun ta ayyana Honarabul Afam Victor Ogene na jam’iyyar Labour a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Faburairu.

Kotu ta yi fatali da korafin PDP, ta bai wa LP nasara a Anambra
Kotun Zabe Ta Yi Fatali da Korafin PDP, Ta Bai Wa LP Nasara. Hoto: Afam Victor Ogene.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke tsakanin LP da PDP?

Ogene yayin da ya ke martani ya bayyana nasarar a matsayin bukatar al’umma, ya godewa ubangiji da wannan nasara daya ba shi, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Zaben Gamnan Kogi: Tashin Hankali Yayin da Magoya Bayan APC Da SDP Suka Yi Musayar Wuta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalai uku na kotun da ke zamanta a Awka babban birnin jihar Anambra sun kori karar Onyema inda su ka ce ba ta da madogara.

A sakamakon da hukumar zabe ta INEC ta fitar a watan Afrilu bayan kammala zaben da ba a karasa ba, ta ayyana Ogene a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sakamakon zaben ya nuna cewa dan takarar jam’iyyar LP ya samu kuri’u 10,851 yayin da abokin hamayyarsa na PDP ya samu kuri’u 10,619.

Har ila yau, dan takarar jam’iyyar APGA a zaben Arinze Awogu ya zama na uku a zaben da kuri’u 10,155.

Wane martani Ogene ya yi kan nasarar LP?

Yayin da ya ke jawabi bayan sanar da hukuncin kotun, Ogene na jam’iyyar LP ya yi godiya ga ubangiji da ya ba shi damar wakiltar wannan mazaba.

Kara karanta wannan

Abu Ya Lalace, An Dakatar da Shugaban APC Kan Zargin Yi wa ‘Yar Shekara 14 Ciki

Ya ce:

“Ina son na yi godiya ga ubangiji da ya ba ni wannan dama da kuma kunyata makiya da su ke son kawo cikas a wannan sakamako.
“Ina kuma son godewa mutanen mazabar Ogbaru ba tare da nuna bambancin siyasa ba da irin jajarcewarsu da addu’o’i na ganin mun samu wannan nasara.”

Ya ce wannan nasara za ta kara masa kwarin gwiwa na ganin ya inganta rayuwar wannan mazaba da su ka zabe shi, Tribune ta tattaro.

Kotu ta rusa nasarar kakakin majalisa a Gombe

A wani labarin, kotun kararrakin zabe a jihar Gombe ta rusa nasarar kakakin majalisar, Abubakar Luggerewo.

Luggerewo wanda dan jam'iyyar APC ne ya rasa kujerar bayan Ahmed Gaddafi na jam'iyyar PDP ya maka shi a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel