Wanene Samuel Anyanwu? Abubuwa 5 Game Da Dan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Imo
- Gabanin zaben gwamnan jihar Imo, Sanata Samuel Anyanwu ya tabbatar da cewa shi ne dan takara mafi karfi, wanda zai lashe zaben jihar
- Tarihin jihar Imo ba zai manta da irin tasirin da Anyanwu ya yi a fagen siyasar jihar na tsawon shekaru ba
- Anyawu ya yi wa 'yan Imo hidima a mukamai daban-daban, da suka hada rike matsayin shugaban karamar hukuma, da kuma dan majalisar jiha da na tarayya
Jihar Imo - Sanata Samuel Anyanwu, ya kasance fitaccen jigo ne a siyasar Najeriya, wanda ya shahara wajen jajircewa kan yi wa al’umma hidima da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban jama'arsa.
Gudunmawar da ya bayar a fagen siyasa da na taimakon jama’a, na nuni da yadda ya ke da himma wajen inganta rayuwar al’ummar da ya ke wakilta, wanda hakan ya sa ya yi fice a fagen siyasar Najeriya, musamman a jihar da ya fito.
Sanata Anyawu dai jigo ne da ake damawa da shi a jam’iyyar PDP, kuma ya zama dan takarar jam’iyyar a zaben gwamna da za a gudanar a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.
Ga muhimman bayanai biyar da ya kamata ku sani game da wannan fitaccen Sanata:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Rayuwa da Ilimi
An haifi Sanata Samuel Anyanwu ranar 18 ga watan Yuni, 1965, a jihar Imo ta Najeriya.
Ya yi karatu a babbar jami'ar Fatakwal, inda ya samu digiri na farko a fannin Kimiyya.
Sanata Anyanwu ya kuma yi karatun a jami'ar Cambridge (makarantar kasuwancin ta 'Judge') da makarantar Kennedy ta jami'ar Harvard.
Tarin iliminsa ya taimaka wajen bunkasa fahimtarsa game da al'amarin mulki da tsare-tsaren shirye shiryen da za su taimaka wa jama'a.
2. Harkokin Siyasa
Sanata Anyanwu dai ya yi fice a fagen siyasa, inda ya nuna jajircewarsa na wakiltar muradun al’umma.
Anyanwu, ya kasance shugaban karamar hukumar Ikeduru, da ke Yammacin jihar Imo, daga shekarar 2004 zuwa 2007.
Bayan haka, ya taba zama dan majalisar dokokin jihar Imo, daga 2007 zuwa 2015.
Tafiyarsa ta siyasa ta kai ga zabensa a matsayin sanatan a majalisar dattawan Najeriya, mai wakiltar mazabar Imo ta Gabas.
Yayin da yake Majalisar Dattijawa, ya shiga cikin kwamitocin da ke mayar da hankali kan da'a, alfarma, matsayar kan jama'a, hukumar hana fasa kwabri, motsa jiki, da haraji.
A kwanakin baya, ya rike mukamin sakataren jam’iyyar PDP na kasa, kafin ya zama dan takarar jam’iyyar a zaben gwamnan jihar Imo.
3. Tallafa wa Al'umma da samar da ayyukan ci gaba
Bayan harkokinsa na siyasa, Sanata Anyanwu ya samu karbuwa saboda ayyukan alheri da jajircewarsa na samar da ci gaba ga al’ummarsa.
Daga ba da tallafin ilimi da kiwon lafiya, zuwa tallafa wa kananun 'yan kasuwa, ya kuma nuna muhimmancin taimakekeniya a tsakanin jama'a.
4. Nasarori a zauren majalisa
Sanata Samuel Anyanwu, ya bayar da gudunmuwa sosai ga harkokin majalisa a matsayinsa na dan majalisa.
Ya kasance yana yin muhawara da tattaunawa kan batutuwan da suka shafi ci gaban tattalin arziki, zuwa yin adalci ga rayuwar jama'a.
Nasarorin da ya samu a majalisar, sun hada da bayar da shawarwari kan samar da ayyukan yi, samar da ababen more rayuwa, da inganta harkokin kiwon lafiya a mazabarsa.
5. Fadi tashi don bunkasa rayuwar matasa
Sanata Anyanwu ya kasance mai fafutukar kare hakkin matasa da kuma shigar da su cikin harkokin siyasa.
Fahimtar irin karfin da matasa ke da shi, ya sa ya himmatu wajen samar da damammaki na ilimi, shirye-shiryen koyon sana'a, da tallafi ga matasa 'yan kasuwa.
Wa ye zai yi nasara a zaben Imo? Yan Najeriya sun zabi Anyanwu
A zaben ra'ayi da Legit ta gudanar a shafin Twitter, kashi 44.9% na wadanda su ka amsa sun ce Athan Achonu, dan takarar jam’iyyar Labour ne zai lashe zaben, yayin da kashi 37.4 suka zabi Hope Uzodimma na APC.
Asali: Legit.ng