Delta: Gwamna Oborevwori Ya Ziyarci Tsohon Shugaban NUPENG a Asibiti

Delta: Gwamna Oborevwori Ya Ziyarci Tsohon Shugaban NUPENG a Asibiti

  • Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta ya ziyarci dattijon ƙasa kuma babban jigon APC da ke jinya a Asibiti
  • Ya ɗauki nauyin duk wata hidima da kuɗin kula da lafiyarsa, yana mai cewa ya cancanci haka duba da gudummuwar da ya bada
  • Jigon APC kuma tsohon jagoran ƙungiyar ma'aikata NUPENG ya yabawa Gwamna da cewa bai san shi mutumin kirki bane kamar haka

Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya ziyarci dattijon kasa kuma tsohon Sakatare Janar na ƙungiyar NUPENG, Chief Frank Kokori, wanda ke jinya a asibiti.

Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, lokacin da ya je duba jigo.
Delta: Gwamna Oborevwori Ya Ziyarci Tsohon Shugaban NUPENG a Asibiti Hoto: thenation
Asali: UGC

Wannan ziyara ta bazata na zuwa bayan labari ya isa ga Gwamnan cewa babban jigon na fama da rashin lafiya kuma an kwantar da shi a wani asibiti a Owerri, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An sace jami'in INEC, takardar sakamakon zabe sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa

Da yake jawabi yayin ziyarar, Oborevwori ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Delta za ta yi duk mai yiwuwa don taimaka wa tsohon shugaban kungiyar ma'aikatan wajen samun ingantaccen magani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, Kokori ya cancanci kulawa da tallafawar gwamnatin jihar a matsayinsa na babban dattijon ƙasa da ya ba da gudummuwa mai tarin yawa.

Ya yi nuni da cewa, duk da suna da banbancin ra'ayin siyasa, zai tabbatar Cif Kokori ya samu kulawar da ta kamace shi a matsayinsa na babban jigo kuma ɗan jihar Delta.

Meyasa ya kai masa ziyara duk da ɗan APC ne?

Gwamna Oborevwori ya ce:

"Na san wasu zasu yi tunanin tun da jigon APC ne ba zan zo na ga halin da yake ciki ba. Ku sani mutanen Delta ne suka zaɓe ni a matsayin Gwamna, don haka wannan ba batu ne na jam'iyya ba."

Kara karanta wannan

Zaben 11 ga watan Nuwamba: Jerin gwamnonin jihar Bayelsa daga 1999 zuwa yanzu

"An yi zaɓe ya wuce yanzu mun zama ɗaya, ko kai ɗan APC ne ko akasin haka, nine dai Gwamnan mutanen Delta gaba ɗaya, saboda haka na zo nan a matsayin Gwamna ba wata jam'iyya ba."

Ya yaba wa Gwamna Oborevwori

Da yake martani, Cif Kokori ya yabawa Gwamna Oborevwori da ya nuna halin Yarabawa, wadanda suke kyautatawa dattawansu ba tare da la’akari da ra’ayin siyasa ba.

Jaridar Vanguard ta rahoto shi yana cewa:

“Ban taba sanin Gwamna Oborevwori mutumin kirki bane sai yanzu domin yana samun labarin halin da nake ciki, nan take ya zo duba ni.
“Shi Gwamna ne na gari, mutum mai zuciyar mutunen kirki kuma na fada masa wasu abubuwa a asirce yadda zai rubuta sunansa a tarihin Najeriya."

Ministan Shugaba Tinubu Ya Shiga Tsaka Mai Wuya

A wani rahoton kuma Tsohon Gwamnan Filato ya shiga tsaka mai wuya kan matsayin da ya kamata ya zaba tsakanin Minista da Sanata bayan hukuncin Kotu.

Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta ayyana Simon Lalong a matsayin zaɓaɓɓen Sanatan Filato ta kudu, ta kori ɗan takarar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel