Zaben Gwamnan Imo 2023: Yan Najeriya Sun Yi Hasashen Wanda Zai Samu Nasara

Zaben Gwamnan Imo 2023: Yan Najeriya Sun Yi Hasashen Wanda Zai Samu Nasara

  • Jihar Imo dai na daya daga cikin jihohi uku da INEC za ta gudanar da zaben gwamna a (yau) Asabar, 11 ga watan Nuwamba
  • Wani zaben ra'ayi da Legit ta wallafa a Twitter ya nuna Athan Achonu na LP a matsayin wanda ya ke kan gaba da kashi 44.9, sai Uzodimma da kashi 37.4
  • Ku lura cewa zaben hasashe ne kawai, kuma INEC za ta bayyana wanda ya yi nasara a hukumance bayan an kammala kada kuri’a

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Owerri, jihar Imo – Imo na daya daga cikin jihohi uku da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) za ta gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

An sace jami'in INEC, takardar sakamakon zabe sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa

Gabanin zaben, ‘yan Najeriya a shafukan sada zumunta sun yi hasashen wanda zai yi nasara a zaben ra'ayi da Legit ta gudanar a shafinta na Twitter.

Yan takarar gwamna a Imo
Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta yanar gizo ta yi hasashen dan takarar jam'iyyar LP Athan Achonu zai lashe zaben gwamna a jihar Imo Hoto: Sanata Samuel Nnaemeka Anyanwu
Asali: Twitter

Bayanai daga INEC sun nuna cewa jam’iyyun siyasa da ‘yan takara 17 ne su ka shiga zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaben Gwamnan Imo: Su wane ne manyan 'yan takara?

Ko da yake, 'yan takara 17 ne za su gwabza a zaben, sai dai 'yan takara uku ne ake daukar su a matsayin manyan 'yan takarar da za su fafata a jihar. Su ne:

  • Hope Uzodimma (APC)
  • Samuel Anyanwu (PDP)
  • Athan Achonu (Labour Party)

Wa zai lashe zaben gwamnan Imo? Anyi hasashen nasarr Athan Achonu

A zaben ra'ayi da Legit ta gudanar a shafin Twitter, 44.9% na wadanda su ka amsa sun ce Athan Achonu, dan takarar jam’iyyar Labour ne zai lashe zaben, yayin da kashi 37.4% suka zabi Hope Uzodimma na APC.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun tarwatsa mata da barkonon tsohuwa kan abu daya tak, sun fadi dalili

A karshe kashi 17.8% na wadanda suka amsa zaben, sun yi hasashen cewa dan takarar PDP, Samuel Anyanwu ne zai zo a na uku.

A lura cewa, wannan zabe, ra'ayi ne kawai da Legit ta shirya domin samar da haske kan yadda zaben jihar Imo zai gudana. INEC ce kadai za ta gudanar da zabe, kuma hukumar zabe za ta bayyana wanda ya yi nasara a hukumance.

Zaben Bayelsa, Imo, Kogi: Jerin manyan laifukan zabe

Kamar dai yadda ya ke a sauran kasashe, Najeriya ma na da dokoki da za su daidaita tsarin zaze da kuma hana aikata laifukan zabe.

Aikata daya daga cikin laifukan zabe na iya jefa mutum cikin fushin 'kuliya manta sabo', gami da dauri idan har laifin ya munana, kamar yadda rahoton Legit Hausa ya nuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel