Kogi: Jimami Yayin da Shahararren Dan Siyasar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Awanni Kadan Kafin Zabe
- Ana saura kwana daya zaben gwamna a jihar Kogi, wani babban dan siyasa ya mutu a safiyar yau Juma’a
- Marigayin, Muhammad Danasabe Muhammed shi ne shugaban karamar hukumar Lokoja babban birnin jihar
- Rahotanni sun tabatar cewa marigayin ya fadi a gidansa a daren jiya Alhamis kafin ya ce ga garinku a safiyar yau Juma’a
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi – Shugaban karamar hukumar Lokoja Honarabul Muhammad Danasabe Mohammed ya riga mu gidan gaskiya.
Wannan na zuwa ne kwana daya tak ya rage a gudanar da zaben gwamnan jihar Kogi a gobe Asabar 11 ga watan Nuwamba.
Yaushe dan siyasar ya mutu a Kogi?
An tabbatar da cewa marigayin ya mutu ne da misalin karfe 4:30 na asuba a asibitin Lokoja babban birnin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta tattaro cewa an dauki Muhammad zuwa asibiti bayan ya fadi a gidansa da ke birnin.
An tabbatar da cewa marigayin a cikin ‘yan kwanakin nan ya kasance kullum a cikin ganawar siyasa yayin da ake shirye-shiryen zabe a jihar.
Wata majiya daga iyalansa ta tabbatar cewa an dauki marigayin zuwa asibitin Shifa bayan faduwarshi a daren Alhamis 9 ga watan Nuwamba.
Mene martanin jam'iyyar APC a Kogi?
Majiyar ta ce:
"Likitoci sun tabbatar da mutuwar marigayin da misalin karfe 4:30 na asubar Juma'a."
Kakakin jam'iyyar APC a jihar, Talba Lakwaja ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Juma'a 10 ga watan Nuwamba, Legit ta tattaro.
Lakwaja ya ce za a binne marigayin da misalin karfe 2 na rana bayan sallar Juma'a a makabartar Unguwar Kura da ke Lokoja a jihar Kogi.
Kungiya ta nemi a kama Melaye
A wani labarin, Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta bukaci a kama Dino Melaye kan zargin ta'addanci a jihar yayin zabe.
Kungiyar na zargin Melaye da aiwatar da ta'addanci a shekarar 2007 yayin zaben Majalisar Tarayya a jihar.
Kungiyar ta ce Dino ya jagoranci ta'addanci wanda ya yi sanadin rasa rayuka da dama a jihar.
Asali: Legit.ng