Zaben Kogi: Yadda Za Ta Kaya Tsakanin APC, PDP da SDP, an Yi Hasashen Mai Nasara

Zaben Kogi: Yadda Za Ta Kaya Tsakanin APC, PDP da SDP, an Yi Hasashen Mai Nasara

  • A ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba ce za a gudanar da zaben gwamna a jihar Kogi
  • An bayyana zaben a matsayin wanda za a kai ruwa rana tsakanin jam’iyyun APC da PDP da kuma SDP
  • Har ila yau, a ranar ce kuma za a gudanar da zaben gwamna a jihohin Bayelsa da Imo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Barista Titilope Anifowoshe ta bayyana cewa nasarar zaben ta ta’allaka ne da kabilar da ta fi sanuwa a jihar da ke Arewa ta Tsakiya.

Yadda zaben jihar Kogi zai wakana tsakanin APC, PDP da SDP
A gobe Asabar za a gudanar da zaben gwamna a jihar Kogi. Hoto: Usman Ododo, Dino Melaye, Yakubu Ajaka.
Asali: Twitter

Su waye za su fafata a zaben Kogi?

Daga cikin manyan-manyan ‘yan takara da za su fafata akwai Usman Ododo na jam’iyyar APC da Dino Melaye na jam’iyyar PDP sai kuma Muritala Yakubu na SDP.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan takarar gwamnan jihar Kogi ya janye ana dab da zabe? Gaskiya ta bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ta ke zantawa da Legit, Anifowoshe ta bayyana cewa kabilun Igala da Ebira ne za su mamayi zaben na ranar Asabar.

Ta ce sauran wadanda za su sauya lamarin zaben akwai kabilun Kabba da Yagba da ke birnin Lokoja a jihar.

Ta kara da cewa tuni aka rarrabe komai a zaben musamman yarukan da su ke da tasiri na yawan jama'a da kuma sanuwa a jihar inda ta ce mutane za su yi nasara.

Wane hasashe aka yi kan zaben Kogi?

Ta ce:

“Ina fatan mutane za su yi nasara a zaben, a fahimta ta zaben an riga an raba ta tsakanin kabilun Igala da Ebira.
“Sai dai Kabba da Yagba da ke Lokoja za su taka muhimmiyar rawa, amma an riga an raba ta tsakanin APC da PDP da kuma SDP.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Fubara ya gana da Wike, Ya ce ‘mai gida na har gobe’

“Babban buri na shi ne zaben ya kasance an gudanar da shi cikin adalci da kuma bai wa kowa dama.”

Kabilar Igala da ke Gabashin jihar sun mulki jihar har na tsawon fiye da shekaru 20 kuma har yanzu su na son ci gaba da rike madafun ikon jihar.

Igala sun fi ko wace kabila yawan jama’a a jihar inda su ke rike da kananan hukumomi 21 a jihar.

Kungiya ta nemi a kama Dino Melaye

A wani labarin, Kungiyar kare muradun al'umma ta nemi a kama dan takarar PDP, Dino Melaye saboda wasu zarge-zarge.

Kungiyar ta nemi a kama Melaye saboda zargin ta'addanci da ake zarginshi a kai a shekarar 2007.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.