Magu ya saduda, ya dauki babban lauyan da zai wakilce shi a gaban kwamitin bincike

Magu ya saduda, ya dauki babban lauyan da zai wakilce shi a gaban kwamitin bincike

Ibrahim Magu, Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arzikin kasa (EFCC) ya dauko hayar babban lauya, Kanu Agabi (SAN), domin ya wakilce shi a gaban kwamitin bincike.

Magu, wanda ake kyautata zaton cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dakatar da shi, ya na fuskantar tuhume - tuhume ma su nasaba da almundahana da kama karya a gudanar da aikinsa na yaki da cin hanci.

A ranar Litinin ne Magu ya fara bayyana a gaban kwamitin bincikensa da aka kafa a fadar shugaban kasa.

Bayan ya bar gaban kwamitin a ranar Litinin, jami'an rundunar 'yan sanda sun yi awon gaba da shi zuwa ofishinsu, inda aka tsare shi har zuwa ranar Talata.

Kafin ya dauko hayar Agabi, lauyan Magu, Oluwatoyin Ojaomo, ya ce masu son ganin maigidansa sun fi annobar korona karfi.

Ojaomo ya bayyana hakan ne a cikin shirin gidan talabijin na Channels yayin da ya ke mayar da martani a kan gayyatar da wani kwamitin shugaban kasa ya yi wa Magu a yau, Litinin.

Lauyan ya ce kwamitin bincike ya gayyaci Magu ne domin ya yi bayani a kan gibin da aka samu a adadin kudin da EFCC ta saka a aljihun gwamnati da kuma wanda Magu ya sanar a bainar jama'a.

A cewar Lauyan, adadin kudin da Magu ya mayar aljihun gwamnati sun zarce adadin kudin da ya sanar EFCC ta kwace.

Magu ya saduda, ya dauki babban lauyan da zai wakilce shi a gaban kwamitin bincike
Ibrahim Magu
Asali: UGC

"Idan kana yaki da cin hanci, ka sani cewa cin hanci zai yakeka, cin hanci ya yi karfi sosai, ma su cin hanci sun yi karfi, sun fi annobar korona karfi.

"Yanzu ku duba abinda yake faruwa, sakamakon a yabawa Magu, manyan mutanen da suka yi karfi saboda cin hanci suna kokarin bata ma sa suna ta hanyar amfani da kafafen yada labaran da su ka mallaka," a cewar Ojaomo.

DUBA WANNAN: Sunaye: APC ta samu sabbin mambobin BoT a karkashin Mai Mala Buni

Kazalika, Jaridar Punch ta wallafa cewa an cigaba da tsare Magu a rana ta biyu bayan ya shafe kusan sa'o'i biyar ya na amsa tambayoyi a gaban kwamitin bincike ranar Talata.

An kara mayar da shi wurin da ake tsare da shi da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Talata.

Majiyar Punch ta sanar da ita cewa rundunar 'yan sanda ta na gudanar da wani bincike na daban a kan Magu bayan binciken da kwamitin shugaban kasa ke gudanarwa a kansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel