Kabilanci, Kudi da Abubuwa 10 da Za Su Yi Tasiri a Zaben Kogi Nan da Kwanaki 6
- A ranar 11 ga watan Nuwamban 2023, mutanen jihar Kogi za su tafi kada kuri’arsu domin su zabi sabon Gwamnansu
- Yahaya Bello ya yi shekaru takwas a kan karagar mulki, ya na burin wani mutumin yankinsa ya gaji mulki a hannunsa
- Sauran jam’iyyun adawa sun fito da gaske, su na kokarin ganin mulkin jihar Kogi ya bar hannun mutanen Kogi ta tsakiya
Abin da rahotonmu ya kunsa shi ne abubuwan da ake tunanin za su yi tasiri a zaben Kogi:
1. Kabilanci a Kogi
Tun fil azal, ba a raba siyasar Kogi da kabilanci. Mutanen Igala da su ka fi yawa a jihar, sun dade su na mulki, yanzu dama ta fada hannun kabilar Ebira.
Akwai ‘Yan yammacin Kogi watau Okun wadanda su ke ganin an bar su a baya, daga cikinsu ne aka samu Dino Melaye ya na yin takara a inuwar PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Karfin mulkin APC
Yahaya Bello da APC ne a kan mulki, Gwamnan zai yi bakin kokarinsa wajen ganin ‘dan takaran da ya tsaida ya yi nasara, wannan na da tasiri a Najeriya.
3. Goyon bayan fadar shugaban kasa
Wasu daga cikin ‘yan takaran jam’iyyan hamayya sun bada gudumuwa a yakin zaben Bola Tinubu, rashin samun tikitin APC ya jawo su ka sauya sheka.
Idan jiga-jigan APC ko na-kusa da shugaban kasa su ka goyi bayan takararsu ta bayan-fage, watakila hakan zai iya bata lissafin Gwamna mai barin-gado.
4. Addini da mata a siyasar Jihar Kogi
Kamar kabilanci, watakila lamarin addini ya yi tasiri a jihar mai rinjayen musulmai, sannan wasu jam’iyyu sun ba mata takarar kujerun mataimakan Gwamna.
Muhammad A. Hassan, mutumin Kogi ne wanda mu ka zanta da shi a game da batun zaben.
“Kirista bai taba yin Gwamna ba duk da yawan kiristoci a Kogi, duk wani dangi akwai kirista. Za a nuna kabilanci, amma kiristoci za su hada-kai.”
- Muhammad Hassan
5. Kudi
Siyasa sai da kudi, saboda haka ake ganin za a yi wa wanda bai da dukiya kafa. Legit ta lura ‘yan takara su na ta tara kudin da za ayi amfani da su a zaben.
6. Kogi 2023: Ingancin zaben INEC
A karshe komai ya danganta ne da kokarin da hukumar INEC ta yi wajen shirya zabe mai kyau, idan ba haka ba wanda ya tafka magudi zai iya samun nasara.
7. Tsaro da aikin jami’an tsaro
Kokarin INEC ya danganta ne da gudumuwar da jami’an tsaro su ka bada a zaben. Ana tsoron cewa za ayi amfani da ‘yan bangar siyasa a zaben mai zuwa.
8. Hadin-kan ‘Yan jam’iyya
Yayin da Dino Melaye ya samu hadin-kan jam’iyyar LP, APC ta na bukatar wadanda su ka yi takarar fitar da gwani su marawa ‘dan takaranta baya sosai.
A cikin abokan hamayyar Ahmad Usman Ododo aka samu wanda ya kai shi kotun koli. Babu mamaki wasunsun su ki yi wa APC aiki a zabe mai zuwa.
9. Raba kan kuri’un mutanen Kogi
Baya ga yiwuwar shirya zagon-kasa da makarkashiyar cikin gida, akwai alamun cewa irinsu Accord Party, ADC, SDP za su raba kuri’un APC da PDP a zaben.
“Ina ganin za a raba kuri’un Igala saboda yawan ‘yan takaransu. Har Dino Melaye zai jawo rabuwar kuri’un saboda ya dauko Igala a mataimakiyarsa.”
- Muhammad Auwal Hassan
10. Kaddara
Duk a je-a dawo, kaddara ta riga fata a zaben Gwamnan na Kogi. A irin haka ne Yahaya Bello ya zama Gwamna sa'ilin da Abubuwar Audu ya rasu a 2015.
PDP ta karbe kujerar Sanata a Kogi
A makon jiya ne aka ji labari Kotun daukaka kara ta raba gardama kan kujerar Sanatan Kogi ta tsakiya, yankin da Gwamna Yahaya Bello ya fito.
Kotu ta tabbatar da Natasha Akpoti-Uduagan wanda ita ce 'yar takarar PDP a matsayin wanda ta ci zabe, hakan na nufin an tsige Sanatan APC.
Asali: Legit.ng